Matan da suka tara kuɗi suka sayi motar kai mata haihuwa asibiti a Jigawa

Matan da suka jagoranci karo-karon kudi har suka yi motar kai mata haihuwa a kauyen Jahun

Matan wani kauye da ake kira Bardo a karamar hukumar Taura da ke jihar Jigawa a Najeriya sun yi karo-karon kudi inda suka sayo motar daukar mata masu juna-biyu zuwa asibiti domin haihuwa.

Matan sun samar da kudin ne inda aka sayi motar domin a rinka kai matan kauyen asibiti idan buƙatar hakan ta taso musamman ma haihuwa saboda matsalar sufuri da ake fuskanta a yankin.

Daga kauyen zuwa asibitin Jahun da ake kai matan haihuwa akwai tazarar kilomita 29, kuma kauyen ya kasance a lungu yake ga rashin kyawun hanya saboda ramuka.

Malama Halima Adamu, ita ta jagoranci yadda aka hada kudin da suka sayi motar ta kuma shaida wa BBC cewa, da naira dubu ɗai-ɗai suka tara kudin sayen motar inda suka bukaci kowacce mace a kauyen da ta bayar da nata kudin.

Ta ce: "Da dubu dai-dai duk wata muka rinka tara kudinmu har sai da muka tara naira miliyan guda, a haka muka bayar aka saya mana motar, yanzu ga shi komai dare idan mace ta tashi haihuwa za a dauko motar a kai ta asibiti ta haihu lafiya a kuma dawo da ita lafiya".

"Idan irin wannan tafiya ta tashi ta zuwa asibiti a haihu, to maigidan mai haihuwar zai bayar da naira dubu biyu, a ciki za a sayi mai na Naira 1500, dari biyar kuma sai a bai wa ma'aji ya hada a cikin sauran kudin da muka tara saboda koda wani gyara zai iya tasowa," in ji ta.

Haihuwa a kan hanya

Dagacin kauyen na Bordo Malam Alhassan Haruna, ya shaida wa BBC cewa, yanzu abin da ya rage musu shi ne gwamnati ta karasa gyaran hanyar data fara saboda suna fuskantar matsala.

Ya ce: "Akwai kwazazzabai a hanyar da aka fara aka bar ta ba a karasa ba, ga ramuka, ni kaina saboda ramuka da kwazazzaɓai sai da matata ta haihu a hanyar ba a kai ga karasawa da ita asibiti ba".

Dagacin ya ce shi yasa suke so gwamnati ta daure ta karasa musu hanyar ko sa samu saukin zirga-zirga.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ko gwamnatin jihar ta Jigawa ke yi a kan batun samar da motoci a kauyuka?

Gwamnatin jihar dai ta samar da wani shirin wanda ya maye gurbin shirin motocin haihuwa lafiya wadanda suka lalace.

Dakta Kabir Ibrahim, shi ne sakataren hukumar lafiya a matakin farko na jihar ta Jigawa, ya kuma shaida wa BBC cewa, "A cikin motoci guda 120, sama da 100 sun lalace basa aiki, amma a yanzu cewa duk wata mota dake cikin al'umma a wuraren da suke da wahalar shiga, to zamu iya daukar wannan mota a matsayin motar haihuwa lafiya".

Ya ce, sun wakilta irin wadannan motocin da su rinka daukar mata suna kai su asibiti domin haihuwa musamman a cikin dare.

Dakta Kabir ya ce: "Su wadannan mutanen da za su rinka daukar matan musamman cikin dare su kai su asibiti domin haihuwa, ba kyauta zasu yi ba, domin duk daga inda ka dauko mace aka kaita asibiti domin haihuwa to kana da naira dubu 4".

Sai dai kuma Dakta Kabir ya ce irin wannan tsari ana amfani da shi ne a kananan hukumomi uku ne domin gwaji.

Karin labarai da za ku so ku karanta: