'Da gangan Trump ya boye wa Amurkawa girman cutar korona'

An ji yadda shugaba Trump ke bayyana yadda ya san girma da tasirin cutar, amma sai ya rika boye wa jama'a.
Bayanan hoto,

An ji yadda shugaba Trump ke bayyana yadda ya san girma da tasirin cutar, amma sai ya rika boye wa jama'a.

Wani Dan jarida, kana mawallafin wani littafi da aka fitar ranar Laraba Bob Woodward, ya kwarmata tattaunawar da ya yi da shugaban Amurka Donald Trump tun lokacin da cutar korona ba ta jima da shiga kasar ba.

An ji yadda shugaba Trump ke bayyana yadda ya san girma da tasirin cutar, amma sai ya rika boyewa jama'a.

To sai dai shugaban ya kare matakin na sa, yana mai cewa ya yi hakan ne da zummar kare 'yan kasar daga aukawa rudani.

An kwarmata wani kiran waya da aka yi da shugaban cikin wani sabon littafi da aka fitar, da ke cewa shugaban ya san girman tasirin cutar, amma ya rika boyewa, tare da nunawa al'ummar kasar cewa babu wani abin damuwa game da cutar.

Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Democrat, Joe Biden, ya ce da gangan shugaban ya rika shirga karya.''Ya yi wa 'yan Amurka karya, da gan-gan ya boye tasiri da hadarin cutar tsawon wata da watanni, yana da bayanan hakan, da gayya ya ki sauke nauyin da ke kansa a matsayinsa na shugaban kasa.

Fiye da mutum 1,900,000 cutar ta kashe kawo yanzu, yayin da ta harbi sama da 'yan kasar miliyan shida.