Terwase Akwaza Gana: Yadda 'gagarumin ɗan fashi' ya addabi Binuwai kafin sojoji su kashe shi

Gana Benue State Terwase Akwaza

Asalin hoton, Amadu Mathias

Bayanan hoto,

Terwase Akwaza

Terwase Akwaza da aka fi sani "Gana," mutumin da aka dinga nema ruwa a jallo a jihar Binuwai da ke yankin tsakiyar ƙasar wanda sojoji suka kashe a ranar Talata, an fara sanin sa ne a shekarar 2015 lokacin da gwamnatin jihaer ta yi wa mutum 500 afuwa.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai a ranar Laraba ya nuna kaɗuwarsa kan yadda sojoji suka tare tawagar motocin gwamna, suka kama tare da kashe Terwase Akwaza, da aka fi sani Gana.

Shi ma Gwamna Ortom ya bayyana yadda ya ji a lokacin da yake yi wa 'ƴan jarida bayani kan yadda shirinsa na yin afuwa ke tafiya a yankin Sankera.

Tuni labarin kisan nasa ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya inda aka dinga tattauna shi a shafukan sada zumunta na tuwita, inda a ranar Alhamis aka yi amfani da maudu'in #Gana fiye da sau 98,000.

Ga dai abin da wasu ƴan Najeriyarv ke cewa:

Chris Ososa Asuelime ya rubuta cewa: Mene ne alaƙar Gwamna Ortom da Gana? Me ya sa Ortom ya ji taƙaicin kashe ɗan ta'adda? so PAINED that the TERRORIST got KILLED? If only Nigerians knows those behind insecurity!

Shi ko A j e b o r@michael_asah cewa yake:

''Gana ya mutu da magana taf a bakinsa. Da gangan aka kashe shi. ''

Akwu N'Esi Obi Ike @Uzomaka_Kelechi cew yake:

''Kisan Gana bai yi ma'ana ba sam-sam idan dai har an yi masa afuwa. Me ya sa sojoji za su kashe shi? Ina fatan dai ba za su dinga irin haka wajen ɗaukar rayukan waɗanda ba su ji ba su gani ba. Allah Ya sa yaran Gana kar su yi tunanin ramuwa.''

chubby_kishimi @aishah_ik ko ta rubuta cewa:

''Muna cikin matsala a ƙasar nan, ji yadda mutane ke jin haushi don an kashe Gana, kuma a haka wasu ke son shiga aljanna. Dole ne sai an mayar da komai addini ko ƙabilanci.

Yaushe Gana ya fara ta'addanci?

Babu wasu bayanai da ke bayyana yadda Gana ya fara ayyukan dabarsa, amma sahsen BBC Pidgin ya gano cewa ya fara ne a lokacin da ya je ya yi fashi da makami a yankin ƙaramar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Binuwai.

An fara sanin Terwase Akwaza "Gana" ne a lokacin da Gwamna Samuel Ortom ya yi ƙorafin cewa yana ta'addanci a jihar da kuma jawo matsalar rashin tsaro ga mutanen jihar.

Yayin da aka kasa kama shi, sai gwamnati ta yi masa afuwa amma daga baya ta sake ƙorafin cewa ya koma kan halin nasa a yayin da rashin tsaro ya ci gaba da addabar jihar.

Gana da yaransa ne suka addabi jihar wajen kai munanan hare-hare a yankin Sankera da suka haɗa da Ukum da Logo da ƙaramar hukumar Katsina Ala local a jihar Binuwai.

Munanan ayyukansu sun shiga har jihar Taraba. Sun kai manyan hare-haren fashi da makami da satar mutane don kuɗin fansa.

Ana zargin shi da tawagarsa sun kashe mutane da dama da ba su ji ba su gani ba, da suka haɗa da mataimaki na musamman kan harkar tsaro ga gwamnan Binuwai a cewar hukumomi, kuma kan hakan da wasu manyan laifukan ne jami'an tsaro suka dinga neman su ruwa a jallo.

Gana ɗan asalin ƙaramar hukumar Katsina-Ala LGA na jihar Binuwai. Yana jin harshen Tivi da Idoma da Turancin Buroka.

Afuwar shekarar 2015

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto,

Terwase Akwaza da aka fi sani da "Gana" ya yi ƙaurin suna a Binuwai

A shekarar 2015 ne gwamnan Binuwai a wa'adinsa na farko ya yi afuwa ga wasu mutum 500 da ake zargi da aikata muggan laifuka afuwa, ciki kuwa har da Gana da yaransa da suka addabi jihar.

Gwamnatin na kan shirya karo na biyu na yin afuwar a lokacin da sojoji suka tare tawagar gwamna a hanyar Gbese-Gboko-Makurdi suka kashe.

2016

A shekarar 2016 rundunar ƴan sandan Binuwai ta yi ikirarin cewa Gana da yaransa sun kashe mutum biyar a jihar da suka haɗa da wata mata mai shekara 85, wacce suka harbe ta a wani hari da da suka kai Tor Donga a ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Ƴan danda suna neman sa ruwa a jallo a 2017

A shekarar 2017, rundunar ƴan sanda ta ayyana neman sa ruwa a jallo tare da sanya tukwiwcin naira miliyan 10 ga duk wanda ya kai musu kansa, ko wanda ya bayar da bayanin inda za a same shi.

Asalin hoton, Amadu Mathias

Bayanan hoto,

Wannan hoton an ɗauke shi a wajen bikin miƙa makamansu da suka yi

Ƴan sanda sun ce Gana ya kashe mutum 17 a Zaki Biam da kuma wasu mutum 50 a wurare daban-daban a jihar Binuwai. Sun kuma ce shi ne ya kashe Desen Igbana, mataimaki na musamman ga Gwamna Ortom kan harkar tsaro.

Sun ce ya yi tuban muzuru kan afuwar da aka yi masa ta hanyar komawa ruwan tsundum wajen aikata miyagun laifuka.

Sun ce yaransa ne suka dinga sace mutane da yin fashi da makami da satar shanu da kashe-kashen da aka dinga yi a jihar.

Shirin yin afuwa karo na biyu na 2020

Gwamnatin jihar Binuwai ta ayyana shirin yin afuwa karo na biyu, tare da yin kira ga yaran jaguda da ke yankin Senkera na jihar da su miƙa makamansu.

Gana da gungun yaransa sun je Makurdi don shiga cikin shirin yin afuwa karo na biyu da gwamnatin jihar ke shiryawa gabanin sojoji su kashe shi.