Ƴan bindiga sun sace mutane a Abuja

FCT minister

Asalin hoton, FCTA/twitter

Rundunar ƴan sandan babban birnin Najeriya Abuja ta ce tana kokarin kubutar da mutum biyar da wasu 'yan bindiga suka sace a yankin Gwagwalada.

Mai magana da yawun runudnar ƴan sanda babban birnin Anjuguri Manza ya shaidawa BBC cewa sun kubutar da mutum biyar daga mutanen da ƴan bindigar suka sace a ƙauyen Tungar Maje da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada.

A cewar kakakin 'yan sandan, 'yan bindigar sun tsallaka da mutane biyar din zuwa cikin jihar Neja mai makwabtaka da Abuja.

"A yayin mummunar musayar wutar da aka yi da ƴan bindigar, ƴan sanda sun samu nasarar ceto mutum biyar daga wadanda aka yi garkuwar da su," in ji Anjuguri Manza.

Wasu mazauna garin sun shaida wa da BBC faruwar lamarin inda suka ce tabbatar da cewa ƴan bindigar sun tafi da wasu daga cikinsu.

Adamu Tanko mazaunin Tungar Maje ne ya kuma ce maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe sha biyu na tsakar daren Laraba, inda suka dinga harbe-harbe da bindiga.

Adamu ya ce a lokacin da suka shiga garin mutum 12 maharan suka sace, ''amma jami'an tsaro na ƴan sanda da kuma ƴan banga sun haɗa ƙarfi suka daƙile harin tare da ceto mutum bakwai daga cikin waɗanda aka sace.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shi ma wani ganau Salihu Na'Annabi Isyaku ya ce lamarin ya yi matuƙar tayar musu da hankali, ''don kuwa tun 12 na dare har ƙarfe 3 na tsakar dare ana abu ɗaya,'' in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: ''Maharan da jami'an tsaro sun yi ta yin musayar wuta a tsakanin su, har dai aka samu aka ci galabarsu aka ƙwato mutum bakwai.

''Tun da nake ban taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba a wannan ƙauyen gaskiya,'' a cewar Salihu.

Shaidun dai sun ce maharan ba da ababen hawa suka shiga garin ba, amma sun je da manyan makamai sosai.

Dukkansu sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba amma an ji wa wasu rauni a cewar Adamu Tanko.

Kazalika sun tabbatar da cewa maharan sun kuma fasa wasu shagunan kasuwanci na mutane a garin.

Tungar Maje wani gari ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gwagwalada kuma yana ƙarƙashin Masarautar Zuba ne da ke babban birnin ƙasar Abuja.

Shaidun sun tabbatar da cewa a yanzu haka hankula sun kwanta, sai dai kuma ba a ji ɗuriyar sauran waɗanda maharan suka sace ba zuwa yanzu.