Me ke jawo yawan lalacewar jirgin ƙasa a Najeriya?

  • Nabeela Mukhtar Uba
  • Broadcast Journalist
Jirgin ƙasa

'Yan Najeriya sun cika da farin ciki tun lokacin da aka farfaɗo da sufurin jiragen ƙasa a wasu yankuna ƙasar.

Matafiya tsakanin Abuja da Kaduna na cikin mutanen da suka fi murna da samun ƙarin hanyar sufuri inda suke kai komo a jiragen ƙasa musamman domin gujewa bin titin mota inda ake yawaita sace jama'a.

Lokacin da aka ƙaddamar da jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a shekarar 2016, gwamnatin ƙasar ta sha alwashin inganta shi ta yadda zai yi ƙarko.

Sai dai a baya-bayan nan ana yawan samun rahoton lalacewar jirgin lamarin da kan jefa fargaba a zukatan matafiya da kuma haifar da jinkiri wajen tafiye-tafiye.

A duk lokacin da irin wannan matsala ta faru, ana shafe tsawon lokaci ana gyara lamarin da ke jefa fasinjoji cikin zullumi da fargabar abin da ka je ya zo musamman yadda jirgin zai iya samun matsala a tsakiyar daji.

Shekara huɗu kenan da ƙaddamar da jirgin ƙasan da ke tashi daga Abuja zuwa Kaduna, lalacewar jirgin na ƙara faruwa sai dai a wasu lokutan hukumomi ba su da wani zaɓi sai na aikewa da wani jirgin domin ya ja wanda ya lalace ɗin.

Ko a 'yan kwanakin da suka gabata, rahotannin da muka samu sun nuna cewa jirgin ya lalace fiye da sau ɗaya - wannan kuma babban abin damuwa ne da masu amfani da jirgin ke yawan kokawa a kai.

A ƙasashen da suka ci gaba, zai yi matukar wahala a samu matsalar jirage ko lalacewarsu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ko me ke jawo lalacewar jirgi a Najeriya?

BBC ta tuntuɓi masana game da abin da ke yawan haifar da lalacewar jirgin ƙasa a Najeriya.

Sai dai ba mu samu jin ta bakin hukumomi ba saboda jami'an da muka kira a waya sun ƙi yin magana kan batun.

Wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da wannan matsala sun haɗa da:

Rashin ingancin jiragen

Farfesa Kamilu Sani Fagge, mai sharhi kan al'amuran siyasa a jihar Kano da ke Najeriya, ya ce jiragen da ake sayowa ba sababbi ba ne domin kuwa a wurin da aka sayo su an yi amfani da su har an daina yayinsu.

"Mafi akasari sun wuce wannan tsarin jirgin, don haka tsohon abu ne za a sayar mana a yi gyare-gyare, shi kuwa tsoho tun da ba sabo ba ne duk gyaran da aka yi masa idan anjima kaɗan wannan abubuwan za su yi ta kawo matsaloli," in ji Farfesa Fagge.

Ya ce duk abin da aka yi shi, yana da wa'adin aikinsa, "idan waɗannan shekarun suka cika, ko da a ajiye yake sai ya samu matsala."

Shi ma Bashir Baba Muhammad, ɗan jarida mai zaman kansa a Najeriya, ya ce kusan komai sai an kawo daga ƙasashen waje saboda "ko lauje na yankan ciyawa ba ƙerawa muke yi ba."

Ya ce mafi yawan jiragen da ake kawowa Najeriya "ruɓaɓɓu ne" da aka gama amfani da su a ƙasashen waje.

Ya ce akwai hukumar da gwamnatin Najeriya ta tanada don duba ingancin kayayyaki ta Standard Organization of Nigeria amma an gaza duba ingancin kayayyakin da ake shigowa da su cikin ƙasar.

Amfani da jiragen fiye da ƙima

Farfesa Kamilu Fagge ya bayar da misali da jirgin da ake amfani da shi tsakanin Abuja zuwa Kaduna inda ya ce jiragen ba yawa ne da su ba kuma ana yawan amfani da su har ta kai ya wuce iyakar amfanin da ya kamata a ce an yi da su.

"Misali rayuwar jirgin za a ce bai fi jirgin ya zo Abuja sau ɗaya ya koma ba, ko a cikin mako bai fi ya yi zirga-zirga sau biyu ko sau uku amma mu a nan kullum ya je ya dawo ya je ya dawo, aikin da zai yi a sati ɗaya sai ya yi a rana ɗaya," in ji Farfesa Fagge.

Rashin kishin ƙasa

Bashir Baba Muhammad ya bayyana cewa baya ga rashin sayen abu mai inganci, batun kishin ƙasa ma abin dubawa ne.

Ya ce ƙishin ƙasa shi ne zai sa gwamnati da jama'a su tashi haiƙan wajen samar da abubuwan amfani ga ƙasar ba sai an dangana zuwa ga sauran ƙasashe ba.

Rashin kula da jiragen

Akasarin jiragen a cewar ɗan jarida Bashir Baba tsofaffi ne wanda suke buƙatar kulawa akai-akai.

Rashin ba jiragen kulawar, in ji shi, shi ne ke sa wa jiragen suna tsayawa a hanya.

Farfesa Fagge ya bayyana cewa ba a cika yin gyara don riga-kafi ba, sai abu ya lalace ne ake mai da hankali a gyara.

Asalin hoton, Getty Images

Cin hanci da rashawa

Masanin kan harkokin siyasar ya ce cin hanci na taka rawa sosai ta wannan ɓangare "don ko da wani abu ake buƙata na gyara ko wani abu ya lalace, maimakon a sa mai inganci ko sabo, waɗanda aka ɗorawa nauyin sai su ɗebe wannan kuɗin su ce za su yi maneji."

Bashir Baba Muhammad ya kara da cewa: "Rashawa da cin hanci ta sa idan aka tashi sayen kayayyakin da ake buƙata a nan Najeriya, jami'ai sai su bi baya su karɓi na goro ko ma a yi kaso mu raba."

Rashin ƙwararru

Jirgin ƙasa kamar mota ne a cewar Farfesa Fagge saboda kowane ɓangare nasa akwai ƙwararrun da suka kamata su kula da shi.

"Mu kuwa saboda cin hanci da rashin ƙwarewa sai ka ga mutane kaɗan su ɗin za a sa su yi gyaran ko sun iya ko basu iya ba," a cewarsa.

Ya ce wannan zai sa jirgin ya riƙa samun matsala "yau yana gyara gobe yana lafiya."

Ya batun jirgin ƙasa a wasu ƙasashen duniya?

Binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa a ƙasashen da suke da ci gaba, matsalar jirin ƙasa ko lalacewarsa ta kau amma a Najeriya kuma ake yawan samun lalacewarsu.

Ba ko yaushe ake fuskantar irin wannan matsala ba saɓanin Najeriya da a cikin mako sai a samu afkuwar matsalar fiye da sau ɗaya.

A Kenya da ke gabashin Afirka, irin wannan matsala ta lalacewar jirgin ƙasa bata faruwa.

A birnin London ma, cikin sama da shekara 100 ba a taɓa samun wani lokaci da jirgin ƙasa ya lalace ba.

Haka ma a India, wani ɗalibi ɗan Najeriya da ya yi karatu a can, ya ce a tsawon shekarun da ya yi a ƙasar bai taɓa ganin wani lokaci da jirgin ƙasansu ya samu matsala ba saboda a cewarsa, shi ne hanyar samun kuɗinsu.

Ko a Belarus, hakan batun yake inda wani ɗan Najeriya da ya zauna a ƙasar tsawon shekara bakwai ya ce ko sau ɗaya cikin shekarun da ya yi, bai taɓa gani ko samun labarin lalacewar jirgin ƙasa ba.

A china ma, yana matukar wahala a samu lalacewar jirgi.

Mafita

Farfesa Kamilu Sani Fagge da Bashir Baba Muhammad sun ce mafita ita ce gwamnati ta yaƙi cin hanci da rashawa da ya yi katutu a Najeriya.

Ya kamata a samu wadatattun jiragen ƙasa don ya zamana cewa ba jirgi ɗaya ko biyu ba ne suke yin aikin da ya kamata a ce jirage suna yi.

Bashir Baba Muhammad ya bayyana cewa akwai buƙatar a riƙa samar da jirage masu inganci sannan a riƙa kula da su kuma idan ana wannan a cewarsa, "ba shakka za a zauna lafiya, al'amura za su tafi yadda ya kamata."

A ganinsa, "idan da muna amfani da ilimin da muke da shi mu shiga ƙera wasu abubuwa da muke buƙata, maganar a tafi waje a kawo wani abu wanda yake ba mai inganci bata taso ba."

Ya ce sa kishin ƙasa a zuci ma wani abu ne da zai kawo sauƙi.

Farfesa Fagge ya kuma ce akwai gudummawar da jama'ar ƙasar za su ba da - "idan an ce abu na gwamnati ne da masu aikin da masu hawa sai a wulaƙanta shi a ƙi alkinta shi."