El-Rufai ya rattaba hannu kan dokar yi wa masu fyade dandaƙa

Nasiru El-Rufai

Asalin hoton, Facebook/Nasir el-Rufai

Bayanan hoto,

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya rattaba hannu kan dokar hukunci mai tsanani a kan duk wanda a ka kama da laifin fyade.

Dokar ta ba da damar kisa ko yin dandaka ga duk wanda a ka kama ya yi wa kananan yara 'yan kasa da shekaru sha hudu fyade.

Hakama karkashin dokar za a iya yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai.

Idan a ka kama mace kuwa dokar ta ce za a cire mata wani sashe na al'aura da ake kira Fallopian tube ko kuma a kashe ta.

Nasir el-Rufai ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa tabbas ya rattaba wa dokar hannu.

A makon da ya gabata ne majalisar jihar Kaduna ta amince da kudurin dokar.

Bugu da kari duk baligin da a ka kama da laifin yiwa 'yan kasa da shekara 14 fyade, za a saka sunan shi kundin rajistar wadanda suka aikata fyade tare da wallafa su a kafafen yada labarai.

Kawo yanzu jihar Kaduna ce kawai a Najeriya da ta tanadi hukunci mai tsanani kan masu aikata fyade a Najeriya.

A na samun koke sosai kan fyade a watannin nan a Najeriya a yan watannin nan.

Kuma duk da hukumomi na samun nasarar kama masu aikata fyaden, ba kasafai a ke yanke musu hukunci ba.

Me ke janyo fyaɗe?

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tsananin bukatar yin jima'i - Likitoci sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.

Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.

"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyaɗe suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato wata jarabar matuƙar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."

Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a riƙa yi musu magani tare da da ba su shawarwari.

Taɓin ƙwaƙwalwa - Dr Shehu Saleh shugaban asibitin kula da masu lalular ƙwaƙwala da ke garin Kware a jihar sokoto ya ce matsalar taɓin ƙwaƙwalwa na daga cikin dalilan da ke sa wasu su aikata fyaɗe musamman wadanda ba za su iya bambance abu mai kyau da marar kyau ba, kamar waɗanda ke aikata sata ko fashi da makami.

"Duk za su iya aikata fyaɗe saboda ba su san cewa laifi ne suka aikata ba, saboda ƙwaƙwalwarsu ta juye."

Sai dai Likitan ya ce yawancin masu aikata fyaɗe dama ce suka samu tsakaninsu da waɗanda suke yi wa fyaɗen da kuma mugun halin da ke ransu.

Ya ce akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi ya biya bukatarsa ta samun gamsuwa amma saboda mugun halin da ke ransu ke sa su aikata yin fyaɗe.

Likitan ya ce fyaɗe na iya jefa yaran da aka yi wa cikin damuwa kan mugun abin da aka aikata masu, wanda zai iya shafar ƙwaƙwalwarsu.

"Babban matsalar fyade shi ne yaran da aka yi wa fyaden, yana janyo masu taɓin hankali har ta kai su ma suna yi wa wasu fyaden," in shi Dr Shehu Saleh.