Guguwar Sally: Mutum rabin miliyan sun shiga cikin zulumi

A man wades through a flooded car park in Gulf Shores, Alabama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hundreds of thousands of homes and businesses are reportedly without power

Mahaukaciyar guguwa Sally ta bar kimanin Amurkawa dubu ɗari biyar cikin duhu yayin da mamakon ruwan saman da ta kawo ke mamaye gaɓar tekun Gulf ɗin Mexico da ke gabashin ƙasar.

Karfin iskar ya ragu bayan da ta isa cikin ƙasar a ranar Laraba amma guguwar ta ci gaba da gigita jihohin Florida da na Alabama.

Ambaliya ce babbar matsala a halin yanzu, domin ruwa ya shanye dubban gidaje.

Yayin da guguwar ke kara shigewa cikin kasar ta Amurka, wasu mutum 550,000 da ke da muhallansu a yankin sun rasa hasken lantarki tun daren Laraba.

Guguwar ta Sally na ɗaya daga cikin mahaukatan guguwa da suka yi layi suna shirin afkawa yankin kudu maso gabashin Amurka.

Hotunan ɓarnar da Guguwa Sally ta yi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani jirgin ruwa mai jigilar kaya ya kwace a Pensacola na jihar florida

Wani ƙaramin jirgin ruwa ma ya kwance daga inda aka ɗaure shi, amma an yi sa'a ya maƙale a gabar teku kafin igiyar ruwa ta tafi da shi cikin teku.

Babban jami'in ɗan sanda a Escambia County ya ce yankin bai shirya wa wannan iftila'in da guguwar ta Sally ta kawo ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Motoci manya da ƙanana sun jirkice kuma an rufe hanyoyi da gadoji a Mobile na jihar Alabama

Gwamnan Alabama Kay Ivey ya ce sassa masu yawa a garin Mobile sun ga ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba atarihin yankin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Gabar tekun Gulf na jihar Alabama ya fi shan wuyan guguwar ta Sally

Jihohin Alabama, da Florida da kuma Mississippi duka sun ayyana dokar ta baci gabanin isowar guguwar.