Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto 'sun kashe DPO'

Taswirar jihar Sokoto

Wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Gidan Madi da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Maharan sun kai harin ne a ofishin ƴan sanda a tsakar dare kuma har sun kashe DPO a garin, kamar yadda wasu mazauna garin suka shaida wa BBC.

Wani mazauni garin ya ce suna bacci suka ji ƙarar harbe-harben bindiga wanda ya tayar da su daga bacci.

Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar wa BBC da harin, amma kakakin ƴan sandan jihar, ASP Muhammad Sadiq bai yi ƙarin haske ba musamman game da kashe DPO da ƴan bindigar suka yi.

Baya ga kashe DPO, mazauna garin sun kuma ce ƴan bindigar sun yi awon gaba da wasu mata a garin na Gidan Madi.

Sannan sun kwashi makamai a ofishin ƴan sandan da suka haɗa da bindiga AK47.

"Ƴan bindigar sun mamayi ƴan sandan a lokacin da suke zaune a harabar ofishinsu da suka kawo harin," a cewar wani mazauni garin Gidan Madi.

Matsalar hare-hare ta fara ƙamari a yankin, inda ko a kwanakin baya ƴan bindiga sun kai hari a garin Tangaza bayan harin da suka makwanni uku da suka gabata inda suka sace amarya da wata mai shayarwa.

Jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina sun daɗe suna fama da hare-haren 'yan fashin daji, duk da matakan da gwamnatin Najeriya kan ce tana ɗauka don kawo ƙarshensu.

Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan fashin daji a yankunan jihar Sokoto da ke makwabtaka Zamfara.

Karin labarai masu alaƙa