Breonna Taylor: Jerin baƙaƙen fata da ‘yan sandan Amurka suka kashe

.

Asalin hoton, Getty Images

Kotu a Amurka ta samu wani ɗan sanda da laifi sakamakon harbe Breonna Taylor a farkon shekarar nan yayin wani samame da 'yan sandan suka kai a gidanta.

'Yan sandan sun je binciken ne sakamakon zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Ranar Laraba an harbi 'yan sanda biyu a jerin zanga-zangar da ake yi a birnin Louisville saboda matakin da aka ɗauka na ƙin hukunta masu laifin.

Ga wasu daga cikin jerin lamura da suka yi sanadiyar harbe 'yan Amurka baƙaƙen fata tun daga 2014.

17 ga Yulin 2014: Eric Garner

Asalin hoton, Getty Images

Eric Garner ya mutu ne bayan ya yi kokawa da wani ɗan sandan birnin New York, ana zargin Mista Garner ne da sayar da taba sigari ba bisa ƙa'ida ba.

Bayan an shaƙe wuyan Mista Garner, ya dinga furta cewa "Ban iya numfashi" har sau 11.

Lamarin wanda wani da ke tsaye a gefen titi ya naɗa a wayarsa - ya jawo zanga-zanga a faɗin ƙasar. Ɗan sandan da ya yi sanadin mutuwarsa daga baya an kore shi daga aiki, amma ba a ɗauki wani mataki a kansa ba.

Hakan kuma ya faru ne kusan shekara guda bayan da aka fara zanga-zangar Black Lives Matter sakamakon martani kan sakin da hukumomi a ƙasar suka yi wa wani mutum da ya kashe wani matashi Trayvon Martin a Florida.

9 ga Agustan 2014: Michael Brown

Asalin hoton, Getty Images

Wani ɗan sanda ne ya kashe Michael Brown, ɗan shekara 18 a birnin Ferguson da ke Missouri, inda ɗan sandan ya ce ya ji labarin Mista Michael, wanda bai ɗauke da makami ya saci kwalin sigari.

Takamaiman abin da ya faru har Michael ya mutu babu tabbaci a kai, sai dai an harbi Mista Michael ɗin har sau shida, kamar yadda binciken likitoci ya bayyana.

Ɗan sandan da ya yi kisan daga baya ya ajiye aikinsa, amma kuma ba a yanke wani hukunci a kansa ba.

Lamarin ya jawo zanga-zanga daban-daban da kuma tayar da zaune tsaye a Ferguson, kuma hakan ya ƙara zafin zanga-zangar Black Lives Matter.

22 ga Nuwambar 2014: Tamir Rice

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tamir Rice, wani yaro ne mai shekara 12, wanda aka harba a Cleveland, kuma wani ɗan sandan jihar Ohio ne ya harbe shi sakamakon wani rahoto da ɗan sandan ya samu kan cewa wani yaro na bin mutanen da ke wucewa kan titi da bindiga, bindigar ma da a ake zargi ba ta gaske bace.

'Yan sandan sun bayyana cewa sun faɗa wa Rice ya ajiye makaminsa - amma a maimakon ya ajiye bindigar, sai ya nuna wa 'yan sandan bindigar kamar zai harbe su.

Sai da 'yan sandan suka kashe Rice tukuna suka tabbatar da cewa bindigar da yake ɗauke da ita ta wasa ce.

Babu wanda aka hukunta bayan faruwar wannan lamarin. Bayan shekara uku da faruwar abin ne aka kori ɗan sandan daga aiki sakamakon samunsa da laifin yin ƙarya a fom ɗin da ya sa hannu a kai kafin a ɗauke shi aiki.

4 ga Afrilun 2015: Walter Scott

Walter Scott was shot in the back five times by a white police officer, who was later fired and eventually sentenced to 20 years in prison.

Mr Scott had been pulled over for having a defective light on his car in North Charleston, South Carolina, and ran away from the police officer after a brief scuffle.

The killing sparked protests in North Charleston, with chants of "No justice, no peace".

Wani ɗan sanda ne ya harbi Walter Scott a baya har sau biyar, wanda daga baya an kori ɗan sandan kuma har aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 20.

Lamarin ya faru ne a Arewacin Charleston da ke Kudancin Carolina inda ɗan sandan ya fito da Mista Scott daga motarsa sakamakon fitilar motarsa ba ta da kyau.

Bayan gardama tsakaninsu, sai Mista Scott ya gudu. Kisan da aka yi masa ta jawo zanga-zanga matuƙa inda masu zanga-zangar ke cewa "babu adalci ba zaman lafiya".

5 ga Yulin 2016: Alton Sterling

Mutuwar Alton Sterling ta sa an shafe kwanaki ana zanga-zanga a Baton Rouge da ke Louisiana. An kashe Mista Sterling ne bayan 'yan sanda sun samu rahoton cewa ana samun hayaniya a waje wani shago.

Asalin hoton, Reuters

An naɗi duka abin da ya faru a waya kuma aka baza a shafukan intanet.

'Yan sandan biyu da suka aikata kisan ba a kama su da wani laifi ba, sai dai an kori guda, ɗayan kuma an dakatar da shi daga aikin.

6 ga watan Yulin 2016: Philando Castile

An kashe Philando Castile ne a lokacin da ya fita yawo a mota da budurwarsa a St Paul da ke jihar Minnesota.

Asalin hoton, EPA

'Yan sanda ne suka jawo shi daga cikin motar ya yin da suke wani bincike, inda ya ce musu yana da lasisin riƙe bindiga bayan sun kama shi da ita a wurinsa.

Sun harbe shi a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ɗauko lasisinsa, kamar yadda budurwarsa ta bayyana.

Ta ɗauki lamarin kai tsaye a Facebook, haka kuma an wanke ɗan sandan da aka samu da laifi daga duk wasu zarge-zarge na kisan kai.

18 ga Maris ɗin 2018: Stephon Clark

An kashe Stephon Clark bayan an harbe shi aƙalla sau bakwai a Sacramento da ke California, rahotanni sun ce wasu 'yan sanda ne da suke bincike kan fashi a wani gida ne suka aikata aika-aikar.

Babban lauyin gundumar ya bayyana cewa 'yan sandan ba su aikata wani laifi ba, sakamakon 'yan sandan suna ƙoƙarin kare kansu don suna tunanin Mista Clark na ɗauke da bindiga.

Wayar salula kaɗai aka gano a wurin da lamarin ya faru.

Bidiyon da aka yaɗa a shafukan intanent na yadda lamarin ya faru ya jawo zanga-zanga matuƙa.

25 ga Mayun 2020: George Floyd

Asalin hoton, Getty Images

George Floyd ya mutu ne bayan da aka kama shi a Minneapolis, inda 'yan sanda suka murƙushe shi, inda ɗaya daga cikin 'yan sandan ya yi amfani da gwiwar ƙafarsa ya ɗorata kan wuyan Mista Floyd.

A lokacin, Mista Floyd ya ta ihun cewa bai iya numfashi.

An ta gudanar da zanga-zanga a jihohin Amurka, hakazalika, an yi zanga-zanga a ƙasashe daban-daban na duniya.

An samu ɗaya daga cikin 'yan sandan da laifin kisa ba dagangan ba, haka kuma sauran ukun za su fuskanci hukuncin taimakawa wurin aikata kisa,