Fafaroma ya ki ganawa da Mike Pompeo a Vatican

Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Fadar Vatican ta ki amincewa da bukatar sakataren harkokin wajen Amurka na ganawa da Fafaroma Francis.

Fadar ta sanar cewa ba ta karbar bakuncin 'yan siyasa a lokacin yakin neman zabe.

Matakin fadar ya fama rikicin diflomasiyya da ke tsakanin Amurka da China, bayan kalaman Mike Pompeo kan alakar China da cocin Katolika.

Kan haka fadar Vatican ta zargi Mista Pompeo da cewa yana son amfani da irin wadannan kalamai ne don samun kuri'ar Amurkawa a zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.

A farkon watan Satumba ne Mista Pompeo yace cocin Katolika na ganganci da kimar da ya ke da ita, bayan da cocin ya sabunta yarjejeniya da China kan nadin wasu malaman coci.

Donald Trump na samun goyon bayan kungiyoyin masu tsatstsauran ra'ayin addinin Kiristanci da su ka hada da wasu mabiya darikar Katolika, da ke ganin cewa Fafaroma Francis ya cika sassauci.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zargin a na muzgunawa mabiya darikar Katolika a China, saboda kulla alaka da Fafaroma Francis a maimakon kungiyar mabiya darikar Katolika da ke Chana.

To amma hakan bai sa fadar Vatican ta fasa kulla yarjejeniya da Chinar ba a shekarar 2018, ta samun damar fada a ji kan nadin malaman cocin a kasar.

Jaridar AFP ta ambato Cardinal Parolin, daya daga cikin masu bai wa fadar Vatican shawara kan diflomasiyya na cewa Fafaroma ba ya karbar bakuncin manyan yan siyasa yayin da a ke dab da zabe.

Haka ma Mista Parolin ya ce ba abin mamaki ba ne Mike Pompeo na kalamai kan cocin Katolika da nufin jan ra'ayin mabiya darikar su zabi mai gidansa.

Ya kuma ce alakar Fadar Vatican da China ba ta shafi Amurka ba ta kowace hanya.