Félicien Kabuga: Wata kotun Faransa ta ce ana iyayi ma sa shari'a a gida

Interpol handout photos of Félicien Kabuga

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Félicien Kabuga - daya daga cikin attajiran Rwanda a shekarun baya, yayi amfani da sunayen bogi 28 doimn boye asalin sunansa.

France's top appeals court has agreed to extradite the alleged financier of the Rwandan genocide, Félicien Kabuga, to face trial in Tanzania.

Mr Kabuga, in his 80s, was arrested in May at his home outside Paris after 26 years on the run.

Some 800,000 people were killed in the 1994 genocide.

Mr Kabuga is alleged to have funnelled money to militia groups as chairman of the national defence fund. He denies all the charges.

During a court appearance in May, he described the accusations as "lies".

His lawyers had argued that he was too frail to be sent to face trial at the UN tribunal in the Tanzanian town of Arusha.

Wata babbar kotun daukaka kara a Faransa ta yanke hukunci cewa masu shigar da kara na iya mayar da Félicien Kabuga gida Afirka domin a yi ma sa shari'a kan kisan kiyashin Rwanda wanda ake tuhumarsa da hannu dumu-dumu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mista Kabuga mai shekara 80 da wani abu na cikin manyan mutanen da ake tuhuma da amfani da arzikinsa wajen iza mutane suka aikata ayyuakan assha.

An kama shi a birnin Paris ne a watan Mayu a gidansa da ke birnin bayan ya shafe shekara 26 yana buya.

KImanin mutum 800,000 ne aka kashe a rikicin da ya zama na kisan kiyashi a Rwanda a 1994.

Ana tuhumar mIsta Kabuga da tura kudade ga kungiyoyin 'yan sa kai a matsayins ana shugaban hukumar da ke kula da asusun tsaro na kasar Rwanda. Ya musanta tuhumar da ake ma sa.

Yayin shari'ar da aka fara yi a wata kotun cikin watan Mayu, Mista Kabuga ya kira tuhume-tuhumen "karairayi".

Lauyoyin da ke kare shi dai sun so a bar shi a Faransa a madadin mayar da shi kotu ta musamman ta Majalisar Dinkin Duniya da ke yi wa wadanda ake tuhuma da aikata manyan laifuka kamar na yaki sharia'a.

Kotun na birnin Arusha na kasar Tanzania ne, kuma a can za a kai Mista Kabuga da zarar an kammala zaman da wannan kotun ta Faransa ke yi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An gano Félicien Kabuga yana boyewa cikin wani gida cikin wannan unguwar mai suna Asnières-sur-Seine a birnin Paris