Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Dembele, Vinicius, Jovic, Brewster

Ousmane Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta soma tattaunawa da Barcelona kan karbo aron dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, a cewar jaridar. (Mirror)

Tottenham ta kusa kammala kulla yarjejeniya domin karbo aron dan wasan Benfica da Brazil mai shekara 25 Carlos Vinicius, wanda kudin da za a biya kafin a sake sh ya kai £89m. (Mail)

Wakilin dan wasan Real Madrid Luka Jovic, mai shekara 22, ya ce dan wasan na Serbia yana son tafiya Manchester United, a yayin da Inter Milan da Roma suke zawarcinsa. (Star)

Liverpool na shirin amincewa da £23m daga wurin Sheffield United kan dan wasan Ingila mai shekara 20 Rhian Brewster.(Sun)

Manchester United ta musanta rahotannin da ke cewa tna son dauko dan wasan Ingila mai shekara 23 Ainsley Maitland-Niles, wanda zai iya murza leda a matsayin mai tsaron baya, daga Arsenal. (Manchester Evening News)

Chelsea za ta iya sayar da dan wasan Sufaniya Marcos Alsonso, mai shekara 29, da dan wasan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, da kuma dan wasan Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 24, kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan kwallo. (Star)

Arsenal na tattaunawa domin bayar da aron dan wasan Faransa mai shekara 21 Matteo Guendouzi ga Marseille. (Telefoot, via Express)

Kazalika Arsenal ta samu tagomashi a yunkurinta na dauko dan wasan Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar daga Lyon, a yayin da kocin kungiyar Jean-Michel Aulas ya ce za su iya "rasa 'yan wasa biyu" kafin wa'adin musayar 'yan kwallo ya cika. (Metro)

Newcastle United za ta fafata da Valencia a yunkurin dauko dan wasan Juventus da Italiya mai shekara 26 Daniele Rugani, wanda ake rade radin zai tafiFulham, West Ham ko kuma Sevilla. (Sportitalia, via Football Italia)