Musulman Indiya sun ce an fara kai su bango kan takura musu da ake yi

Musulmai a Indiya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Akasarin Musulan Indiya na aiki a ƙananan ma'aikatun da ba su da ƙarfin tattalin arziki a kasar

Kusan shekaru 30 da suka gabata duk da shaidu 850, sannan daga bisani fiye da kasidu 7,000 da hotuna da faya-fayen bidiyo da aka gabatar, wata kotu a Indiya ba ta samu kowa da aikata laifin rushewa tare da banka wuta a wani masallacin da aka gina tun a ƙarni na 16 a kasar ba, wanda wasu gungun mutane mabiya addinin Hindu ne suka kai hari a masallacin da ke birnin Ayodya mai daraja.

A cikin mutum 32 da ake zargi da yanzu haka suke a raye, akwai tsohon mukaddashin Firimiya LK Advani, da sauran jiga-jigan jam'iyyar BJP.

A hukuncin da aka yanke a ranar Laraba, kotuna ta wanke duka waɗanda ake zargin, inda ta ce wasu ne da ba a san ko su wane ne ba suka kai harin tare da lalata masallacin a shekara ta 1992, ba wai an kitsa shi ne da gangan ba.

Hakan ya faru duk kuwa da ɗumbin sahihan shaidun da suka gane wa idanunsu yadda aka rushe ginin masallacin, wanda ya dauki sa'o'i kadan, da ya nuna cewa sai da aka tsara aka kuma aiwatar, ba kuma tare da tunanin abinda zai biyo baya ba, wanda a kan idon wasu jami'an 'yan sanda ne a kuma gaban dubban jama'a.

A shekarar da ta gabata ne kotun ƙolin Indiya ta tabbatar da cewa harin ''tsararre ne'' kana ''mummunan karya dokar kasa ce''

Ga baki daya ana ɗaukar sakamakon wannan hukunci a matsayin wani rauni da gurɓacewa a ɓangaren shari'a na kasar ta Indiya.

Wasu ma na fargabar cewa lalacewar ta kai ta yadda ba zai gyaru ba saboda yawan shisshigin manyan 'yan siyasa, da rashin mayar da hankali wajen inganta ɓangaren shari'ar.

Amma kuma za a iya cewa sakamakon hukuncin ya fito fili ya nuna damuwar da ake da ita na ƙaruwar nuna bambanci da wariyar da Musulman Indiya miliyan 200 ke fuskanta a kasar.

A karkashin gwamnatin jam'iyyar BJP ta Narendra Modi, tura ta kai bango ga wasu al'ummomi inda suke jin cewa ana cin mutuncinsu fiye da ma a ko wane lokaci a cikin tarihin mulkin wadancan gwamnatocin Indiya da suka shude, inda suke yaba wa dimokraɗiyya mafi girma a duniya tun bayan samun 'yancin cin gashin kan kasar a shekara ta 1947.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Musulmai kimanin 200 ne a kasar Indiya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Gungun 'yan daba sun sha kashe Musulmai a kan cin naman saniya ko kuma jigilar shanu, wadanda masu bin addinin Hindu ke dauka a matsayin abin bauta.

Gwamnatin Mr Modi ta yi garanbawul ga dokokin da za a bi diddigin 'yan gudun hihjirar da ba Musulmai ba da suka shigo daga kasashe maƙwabta.

Ta rarraba jihar Jammu da yankin Kashmir da Musulmai suka fi rinjaye, kana ta raba su da 'yancin cin gashin kai da kundin tsarin mulki ya tanadar musu.

A cikin wannan shekarar an zargi Musulmai su kadai da yada cutar korona bayan da 'yan wasu kungiyar Musulman suka halarci wani taron adddinin Musulunci a birnin Delhi.

Amma kuma tarukan addinin Hindu da ake gudanarwa lokacin wannnan annoba ba su taba cin karo da irin wadannan zarge-zarge ko dora laifin da ba nasu ba, ko suka a kafafan yada labarai ba.

Ba ma a nan batun ya tsaya ba, an sha yin awon gaba da dalibai Musulmai da masu fafutika ana garkame su a gidan kaso kan zargin haddasa fitina kan dokar zama dan kasa a birnin Delhi lokacin hunturun da ya gabata, yayin da mabiya addinin Hindu da suka haddasa hargitsin ba a yi musu komai ba.

Musulmai da dama na kallon sakamakon hukuncin na Babri a matsayin wani ci gaba da cin mutuncinsu ne.

Batun nuna wariya ya fito fili. Jam'iyar Mr Modi ta tabbatar da aƙidar mabiya addininta na Hindu.

Manyan kafafen yada labaran kasar kan fito fili suna ɓata sunan Musulmai. Jam'iyyu da dama na Indiya da a baya suke da tagomashi da suka taɓa mara wa al'ummar Musulman baya, yanzu haka sun juya musu baya.

Masu suka sun zargi babbar jam'iyar adawa kan amfani da Musulman wajen samun ƙuri'u ba tare da yi musu abinda ya dace ba.

Ita kanta al'ummar Musulman shugabanninsu da ya kamata su fito su yi magana da yawunta ba su da yawa.

"Musulmai sun yanke ƙauna da lamarin gwamnatin. Suna ganin an kai su bango, kana jam'iyyun siyasa da ma'aikatu da kafafen yaɗa labarai sun gaza a taɓuka musu komai.

Akwai rashin kwarin gwiwa a cikin al'ummar,'' in ji Asim Ali, wani masani a wata cibiyar bincike kan manufofin gwamnati da ke birnin Delhi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Musulmai masu zanga-zanga akan dokar zama dan kasa a shakarar bara

A gaskiya, Indiya na da dadaɗɗen tarihin nuna wariya ga al'ummar Musulmai. ''Ana daukarsu marasa kishin kasa'', kamar yadda wani rahoto ya nuna.

Amma a wata daban kuma, yayin da Indiyawa da dama ke kallon ba a yi wa Musulamai adalci, al'ummar ''Musulman ba su ci gajyar komai daga al'amuran da suka shafi zamantakewa da tattalin arzikin kasar ba'', kamar yadda wasu masanan tarihi suka bayyana.

An cunkushe Musulmai da daman gaske a yankuna da unguwannin marasa galihu a cikin manyan birane.

A shekara ta 2016, kason da suka samu na yawan jami'an ƴan sanda a yankunan nasu kasa da kashi 3% ne, yayin da yawan al'ummar Musulman ya kai kimanin fiye da kashi 14% na yawan al'ummar kasar ne.

Kana kashi 8% kacal na Musulman da ke manyan birane ne ke yin aikin da ake biyansu albashi akai-akai.