Nigeria @60: Hotunan ƴan Kannywood na murnar cikar Najeriya shekara 60

Ga wasu hotuna na wasu fitattun taurarin Kannywood da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta albarkacin ranar cikar Najeriya shekara 60 da samun ƴanci.

Dukkansu sun sanya tufafi launin tutar Najeriya, wato kore da fari.

Asalin hoton, Ali Nuhu IG

Bayanan hoto,

Ali Nuhu wanda aka fi kira da Sarkin Kannywood, ya wallafa wannan hoton tare da cewa: ''Ƴancin kai da ƴanci na gaskiya kan samu ne kawai ta hanyar yin abin da ya dace. A matsayinmu na ƴan Najeriya, ƙasarmu da muke ƙauna, muna buƙatar yin abin da ya dace don ganin sauyin da ko yaushe muke magana a kansa ya samu. Ƙasarmu ta cika shekara 60, dole mu yi fafutuka a tare don tabbatar da martabarta.''

Asalin hoton, Washa IG

Bayanan hoto,

Fati Washa kuwa cewa ta yi: ''Ku zo mu ɗaga hannu don murnar wannan ranar tare da yin bikinta. Ku zo mu tashi tsaye don nuna girmamawarmu ga jagororin da suka mutu a fafutukar nemo mana ƴanci. Ku zo mu rera taken ƙasarmu ɗauke da tutoci a hannayenmu don bikin wannan rana mai muhimmanci.''

Asalin hoton, Sani Danja

Bayanan hoto,

Shi ma tauraro Sani Danja ya wallafa wannan hoton ne tare da wasu yara inda ya ce: ''Yaranmu na yau, shugabannin gagarumar ƙasarmu Najeriya. Barka da zagayowar ranar samun ƴancin kai Najeriya.''

Asalin hoton, Mansura IG

Bayanan hoto,

Yayin da matarsa Mansurah Isah kuwa ta wallafa wannan rangaɗeɗen hoton tare da cewa: ''Babu wani waje da ya kai gida. Barka da zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya.''

Asalin hoton, Sadiq Sani

Bayanan hoto,

Fitaccen jarumi Sadiq Sani Sadiq ya rubuta cewa: ''Nigeria ƙasarmu ta gado. A cikinki aka haife mu a cikinki muka girma, ba mu da wata ƙasa da ta fi ki, a kullum muna alfahari da ke. Mun sani Allah ya albarkace ki da ɗumbin dukiya mai tarin yawa domin mu amfana, amma Kash! Allah ya jarrabe mu da shugabanni mafi yawan su azzalumai marasa kishin kasarsu, mu kuwa talakawan akasarin mu ba mu da godiyar Allah. Ke dai ga ki nan shekararki 60, amma kina nan ba ki canza ba, muna rokon Allah ya ba mu ikon sauya halayenmu da mu da shugabannin kasarmu baki ɗaya. Barka da zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya.

Asalin hoton, Daso IG

Bayanan hoto,

Ita ma Saratu Gidado, sanye da tufafi launin tutar Najeriya ta rubuta cewa: ''Ina yi wa dukkan ƴan Najeriya murnar zagayowar ranar samun ƴancin kan ƙasarmu.

Asalin hoton, Ramadan Booth

Bayanan hoto,

Sai Ramadan booth wanda ya ce: ''Barka da zagayowar ranar samun ƴancin kai Najeriya.''

Asalin hoton, Maryam Yahaya

Bayanan hoto,

Ita ma tauraruwa Maryam Yahaya cewa ta yi ''Barka da zagayowar ranar samun ƴancin kai Najeriya.''