Kalli hotunan iyalan Buhari da na Jonathan a shagalin cikar Najeriya shekara 60

Ga wasu ƙayatattun hotuna na manyan masu ƙasar a lokacin bikin cikar Najeriya shekara 60 da samun ƴancin kai da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.

Shugaba Buhari da matarsa Aisha

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha suna yi wa juna kallon ƙauna, bayan sun ƙure adaka a ranar da Najeriya ke cika shekara 60 da samun ƴancin kai.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

A nan kuma, tsohon shugaban ƙasar ne da Buhari ya kayar a zaɓen 2015 Goodluck Jonathan da mai ɗakinsa Patience da kuma Buhari da tasa gimbiyar suke raha tsakaninsu a Dandalin Eagle Square da ke Abuja, a ranar murnar samun ƴancin kan.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Mata ku ne biki! Nan wasu mata ne ciki har da ƴaƴan Shugaba Buhari wato Zahra da Halima suka ɗauki hoton tare da shugaban da mai ɗakinsa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

A nan kuma masu ƙasar ne dai ciki har da shugabannin majalisun wakilai da dattijai da kuma mataimakin shugaban ƙasa, dukkan su sanye da takunkumi don bin dokoki kare yaɗuwar cutar korona.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Ga dukkan alamu Shugaba Buhari wata magana mai muhimmanci yake yi wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a nan. Daga bayansu a tsaye ga dai Goodluck Jonathan da kuma Ministan birnin tarayya Muhammad Bello.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Soja maganin wani soja! Sojoji ne suke yi wa tsohon janar ɗin soja kuma shugaban ƙasar farar hula na yanzu faretin girmamawa a wajen taron.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Ba jawabai kawai aka gudanar ba, dandalin ya samu halartar masu wasannin ban sha'awa daban-daban. Wasu sojojin Najeriya ne suka nuna bajintarsu a wajen bikin na indipenda. Ashe dai ba ga yaki sojoji kawai suka kware ba.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Wanda ya iya ya huta! Nan wasu mata ne suke cashewa tare da bobboƙarewa duk a cikin mrunar cikar Najeriya shekara 60. Su ma dai sojoji ne.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ke nan ana zagayawa da shi a cikin Dandalin Eagle Square cikin wata mota ƙarƙashin rakiyar sojoji.

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Sojoji sun jeru reras, Shugaba Buhari yana kan mota yana duba su, yana kuma dagawa mahalarta taron hannu.