Kasafin Kuɗin Najeriya na 2021: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08

Buhari Budget

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Buhari ya bukaci 'yan majalisa su amince da kasafin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar - a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai.

Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805.

A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa ke cin karo da shi.

Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe.

Me kasafin zai mayar da hankali a kai?

Asalin hoton, Buhari Sallau

Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ana jimullar kuɗin da gwamnatin tarayya za ta kashe a shekara mai zuwa da ya kai naira tiriliyan goma sha uku, da miliyon dari takwas, wanda ya hada da naira tiriliyin biyar da naira biliyan sittin da biyar da za a kashe a kan harkokin gudanarwa na yau da kullum.

Da albashin ma'aikata da ya ki naira tiriliyon uku da biliyon saba'in da shida, da kuma naira tiriliyan uku da biliyon goma sha biyu na ɗawainiyar biyan bashi.

Wasu hidimomin da za su lashe biliyoyin naira, ciki har da biyan kudin fansho da sauran wajiban da suka rataya ga wuyan gwamnati.

Shugaban Najeriyar ya bayyana cewa an tsara kudurin kasafin kudin ne ta hanyar ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato sai da aka lura da samun gwamnati ta fuskar kudin-shiga, da rance ko bashin da za ta ciwo da kuma tallafin da za ta yi, ko wanda zai shiga hannunta.

Kuma wannan ne ma ya sa gwamnati ta ƙiyasta farashin gangar mai a kan dala 40.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnati ta duƙufa wajen fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci nan da shekara 10 masu zuwa.

Me ya faru a majalisar?

Asalin hoton, Buhari Sallau

Ya gabatar da kasafin ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Alhamis.

Rahotanni sun ce an jibge jami'an tsaro da yawa a harabar Majalisar Dokokin da ke Abuja, inda Shugaba Buharin ya gabatar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa cikin jami'an tsaron da aka kai har da na hukumar tsaro ta farin kaya da ƴan sanda da na hukumar hukumar tsaron farin kaya da kare al'umma wato Civil Defense da na hukumar kare afkuwar haɗura.

Sannan an rage yawan masu shiga cikin majalisar.

An yi zaman majalisar lafiya-lafiya ba tare da wata turjiya daga wajen 'yan majalisar ba, kuma wannan bai ba da mamaki ba, idan aka yi laka'ari da irin dasawar da bangaren zartarwa ke yi da na majalisar dokokin.

Shugaban majalisar dattawa, Senata Ahmed Lawan, ya tabbatar da wa shugaban kasar cewa da majalisar dattawa da ta wakilai duka za su gaggauta zartar da kasafin kudin, kamar yadda suka yi bara.

''Mun yi maka alkawari da 'yan Najeriya cewa mun shirya, kuma mun duƙufa wajen nazari da zartar da kasafin kudin nan da karshen shekara.

''Muna la'akari da cewa yin hakan ya zama wajibi domin mun kawar da yanayin nan na rashin tabbas da ke tattare da aiwatar da kasafin kudi, wanda ya yi illa ga tattalin arzikinmu a shekarun da suka wuce, ta yadda za mu dore da shekarar kasafin kudin aka fi so, mai farawa daga watan Janairu, ya kare a watan Disamba.

Shugaban Najeriyar ya shaida wa 'yan majalisar dokokin cewa, jawabin da ya yi taƙaitacce ne, don haka ma'aikatar kudi ce za ta yi cikakken bayani a kan duk wani ƙabli da badin da kasafin kudin ya ƙunsa.

Tun da farko a ranar Laraba shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Barau Jibril ya ce, gabatar da kasafin kuɗin na wannan shekarar zai sha bamban da na sauran shekaru sakamakon annobar cutar korona.

A cewarsa, za a bi ƙa'idojin kare yaɗuwar cutar da kuma yin tanadi ta yadda ba za a samu cunkoso ba yayin gabatar da kasafin kuɗin, hakazalika ba za a daɗe wurin gabatar da kasafin kudin ba kamar yadda ake yi ba a da.

Asalin hoton, Nigeria Presidency

An dai ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum.

A bara dai an amince da kasafin kudin ne kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 305, haka kuma an saka mizanin gangar man fetur guda a kan dala 57, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 2.18 a kullum.

An sa ran shugaban yayin gabatar da kasafin kuɗin a ranar Alhamis, zai nanata wasu kalaman ministar kuɗin ƙasar wadda ta bayyana cewa ƙudirin kasafin 2021 yana cike da burin bai wa ƙasar damar samun bunƙasa ta kowane ɓangare da kuma zaburar da tattalin arziƙin Najeriya da samar da ayyuka.

Kalaman nata sun kuma haɗa da yauƙaƙa bunƙasar ƙasar, da samar da hanyoyin zuba jari ga ababen more rayuwa, da inganta masana'antu da sana'o'in cikin gida.

Sannan an sa ran wannan kasafin kuɗin na 2021 zai jaddada hasashen samun jumullar kuɗin shiga naira tiriliyan 7.89 da kuma ƙunshin kasafin kamfanoni 60 mallakar gwamnati.

A bara dai, Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2020, wanda ya kai naira tiriliyan 10,594,362,364,830.

Asalin hoton, Buhari Sallau