Ahmed Nuhu Bamalli: Al'adu uku da ake yi kafin sabon sarkin Zazzau ya zauna a fadarsa

New Zazzau Emir HRH Ahmad Nuhu Bamalli

Asalin hoton, Zazzau Emirates/Facebook

Bayanan hoto,

Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kafin nadinsa sarki

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau bayan rasuwar Alhaji Shehu Idris ranar 20 ga watan Satumba na 2020.

Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki.

Ɗa ne ga Nuhu Bamalli, Magajin Garin Zazzau, kuma tsohon minista a Najeriya, wanda ya rasu a 2001.

BBC ta tattauna da Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli wanda shi ne yake rike da sarautar Zuman Zazzau kuma yayan sabon Sarki Ahmed Nuhu Bamalli, inda ya gaya mana al'adu uku da ake yi kafin sabon sarki ya shiga fadarsa.

  • 'Yan majalisar sarki za su yi mubaya'a - A cewar Zuman Zazzau, 'yan majalisar sarki suna yin mubaya'a ne a ranar da aka nada sabon sarki. A al'adance, 'yan majalisar sarkin za su kai caffa da gaisuwa domin yin maraba da sabon sarkin.

"Wannan ne abu na farko da ya zama wajibi da 'yan majalisar sarki za su yi inda za su gaishe da sabon sarki sannan su yi masa mubaya'a," a cewarsa.

  • Ba zai yi zaman fada ba sai bayan an yi masa nadi- Mai girma Zuman Zazzau ya shaida wa BBC cewa sabon sarkin ba zai hau karagar mulki ba sai bayan an yi bikin nadinsa yayin da zai shiga fada bisa rakiyar fadawa, sannan ya karbi sandar sarki.

"Don haka dukkan wadannan kwanaki sabon sarki ba zai shiga cikin inda ake zaman fada ba ko ya zauna a karaga sai bayan an yi bikin nadinsa inda zai karbi sandar girma da kuma tutar masarautar Zazzau wadda ke nuna ya dauki nauyin al'ummar Zazzau a matsayinsa na sabon sarki."

  • Dole a yi nadin sarauta a Zaria- Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli ya ce ba kamar wasu masarautu ba inda za a iya yin nadinsu a babban birnin jiha, ana nada sarkin Zazzau ne a Zaria, ba garin Kaduna ba.

"Mu a nan masarautar Zazzau ana yin nadi ne a Zaria kuma a nan ake yin komai ba a Kaduna ba; gwamna da sauran baki za su zo nan ne domin gudanar da bikin nadin sarkin," in ji shi.

Takaitacce tarihin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli

Asalin hoton, @ahmed_bamalli

Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa da ya hau gadon Sarauta cikin shekara 100, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a 1920.

Shi ne na 19 a jerin sarakunan masarautar.

Ahmad Nuhu Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa, kuma shi ne Magajin Garin Zazzau kafin naɗinsa sarki a ranar Laraba.

Ambasada Ahmed ɗa ne ga Nuhu Bamalli tsohon Magajin Garin Zazzau kuma tsohon minista a Najeriya.

Magajin Garin Zazzau wanda masani shari'a ne da diflomasiyya shi ne jakadan Najeriya a Thailand a yanzu.