Mike Pence: Kalli yadda ƙuda ya zauna daram a kan mataimakin shugaban Amurka

Mike Pence: Kalli yadda ƙuda ya zauna daram a kan mataimakin shugaban Amurka

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A daren Laraba aka yi muhawarar farko ta 'yan takarar mataimakin shugaban kasa a Amurka.

An yi muhawarar ce tsakanin mataimakin shugaban kasa Mike Pence da 'yar takarar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris.

Muhawarar ta fi wadda aka yi tsakanin Donald Trump da Joe Biden nutsuwa.

Amma abin da ya fi jan hankalin wadanda suka kalli muhawarar shi ne ƙudan da ya hau kan Mike Pence.