Bidiyon Zikirin Anfasu na mabiya ɗarikar Ƙadiriyya

Bidiyon Zikirin Anfasu na mabiya ɗarikar Ƙadiriyya

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Babu taƙamaiman adadin mabiya ɗarikar Ƙadiriyya a Najeriya, amma ana ƙiyasin cewa sun kai miliyoyi.

Ɗarikar ta Ƙadiriyya na daga manyan ɗarikun sufaye da ake bi a Najeriya, kuma ana ɗaukanta a matsayin ɗarikar da ta fi daɗewa a ƙasar.

Sidi Abdulkadir Jilani ya rayu ne a birnin Bagadaza na kasar Iraki tsakanin shekarun 1078 zuwa 1166. Yana daga manyan waliyyai da mabiya ɗariƙun Sufaye suke girmamawa, har ma ana masa kirari da sarkin waliyyyai.

Wasu bidiyo da za ku iya kallo