FBI ta bankado shirin yin garkuwa da gwamnar Michigan Gretchen Whitmer

Mrs Whitmer's coronavirus executive orders led to controversy in Michigan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnar Michigan Gretchen Whitmer ta ɓata wa ƙungiyoyn masu adawa da dokar kulle rai

Mahukunta a Amurka sun ce sun dakile wani yunkuri na sace gwamnar jihar Michigan Gretchen Whitmer da kuma hambare gwamnatinta.

Gwamna Whitmer ta yi bakin jin a idon wasu kungiyoyin masu tsattsaurar ra'ayi bayan da ta kaddamar da dokar dakile cuta korona mai tsauri, sai dai wani alkali ya soke dokar a makon jiya.

Jami'an hukumar FBI sun ce mutanen da aka kama sun shirya yi ma ta abin da suka kira shari'ar cin amanar kasa ne kafin a damke su.

Gwamnar ta ce "Bari in yi magana karara - kiyayya, da ta da hankali ba su da matsuguni a babbar jiharmu ta Michigan."

Ta kuma ce, "Duk wanda ya taka doka, ko ya hada kai da wasu domin aikata manyan laifuka kan laifuka, to ya kwana da sanin cewa za mu nemo shi, mu kuma tabbata shari'a ta yi aikinta a kansa."

Asalin hoton, Antrim County Sheriff’s Office

Bayanan hoto,

Layin sama (Hagu - Dama): Adam Fox, Brandon Caserta, Daniel Harris and Kaleb Franks. Daga ƙasa (Hagu - Dama: Ty Garbin, Eric Molitor, Michael Null da William Null

Me suka shirya yi ne?

'Yan sandan FBI na tuhumar mutanen shida wadanda dukkansu mambobin wata kungiyar fararen fata masu ikirarin nuna bambancin launin fata ne da laifin kitsa shirin sace gwamna Whitmer gabanin zaben shugaban Amurka na watan Nuwamba, kuma sun so yin garkuwa da ita a wani boyayyen wuri domin yi ma ta shari'ar kan abin da suka kira 'laifin cin amanar kasa'.

Hukumar ta FBI ta bayyana sunayen mutanen - wadanda dukkansu turawa maza ne - kamar haka: Adam Fox, Barry Croft, Kaleb Franks, Daniel Harris, Brandon Casert da kuma Ty Garbin.

Yayin da ta ke jawabi ga al'umar jihar ta Michigan, gwamna Whitmer ta tuhumi shugaba Trump da ruruta wutar kiyayya a zukatan wasu mabiyansa:

"Shugaban kasarmu ya shafe watanni bakwai da suka gabata yana karyata kimiyya da kwararrun da shi kansa ya nada, kan tasirin annobar korona. Ya kuma shuka rashin jituwa da kiyayya, ban da samar da goyon baya da yake ba wadanda ke neman cusa tsoro da kiyayya da rarrabuwar kawuna."

Ta ce, "A makon jiya shugaban Amurkar ya tsaya a gaban Amurkawa amma ya ki yin Allawadai da kungiyoyin tsirarru na 'yan sa-kai irin wadannan guda biyun na Michigan."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu adawa da dokar kullen da Gwamna Whitmer ta kafa sun riƙa kiranta "Hitler".

Hukumomi sun kama wasu mutum bakwai na daban da laifin ba 'yan ta'addan cikin gidan taimako.

Kungiyar da ake tuhuma ta so ta yi amfani da mutum 200 ne wajen kai hari a ofishin gwamnan jihar ta Michigan, kuma daga nan sun so yin garkuwa da wasu jami'an gwamnati ciki har da gwamna Whitmer.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne gidan Ty Garbin, ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa shirin sace gwamna Whitmer bayan da jami'an FBI suka kai samame can.

Sun kuma so su aiwatar da shirin nasu ne kafin zaben shugaban kasa, amma sun ce idan haka bai samu ba sun shirya bin ta har gida su sace ta kan dokar dakile cutar korona da gwamnatinta ta kafa wanda a ganinsu babban laifi ne da ya shafi 'yancinsu na walwala.