Bidiyon Ku san Malamanku da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Maiduguri

Bidiyon Ku san Malamanku da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Maiduguri

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya, Sheik Sharif Ibrahim Saleh ya ce ya rubuta littatafai fiye da 400 na addinin Musulunci da hannunsa.

Malamin, wanda jigo ne a ɗariƙar Tijjaniya a ƙasar ya faɗi hakan ne a wata hira d aya yi da BBC Hausa a sabon shirinmu na musamman mai taken ''Ku San Malamanku''.

Sheikh Shariff Saleh shi ne shugaban kwamitin fatawa ta addinin Musulunci a Najeriya.