Nancy Pelosi: Tarihin matar da ta jagoranci tsige Donald Trump sau biyu

Nancy Pelosi, mai shekara 80 a duniya, tana da matukar kwarjini a tsakanin 'yan siyasar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nancy Pelosi, mai shekara 80 a duniya, tana da matukar kwarjini a tsakanin 'yan siyasar Amurka

A fagen siyasar Amurka a baya-bayan nan, ana iya cewa shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi na cikin matan da suka fi karfin fada a ji.

Zai yi wuya batun siyasar kasar ya taso ba tare da an ambaci Nancy Pelosi ba kuma a zaben da aka gudanar, ta yi nasarar sake zama kakakin Majalisar Wakilan kasar.

Ita ce macen da ta jagoranci tsige Shugaba Donald Trump sau biyu - da farko a shekarar 2019 sannan a karo na biyu a wannan shekarar ta 2021.

Don haka babu shakka, ba za a daina ganin karfin ikon Misis Pelosi ba, duk kuwa da cewa a yanzu Kamala Harris, mataimakiyar shugaban kasa mai jiran gado ta danne matsayin mace mafi karfin iko a Amurka.

Amma Pelosi, mai shekara 80, za ta ci gaba da taka muhummiyar rawa a sabuwar gwamnatin Joe Biden.

Wace ce Nancy Pelosi?

An haifi Nancy D'Alesandro ranar 26 ga watan Maris a shekarar 1940.

Iyayenta 'yan siyasa ne inda mahaifinta ya taba yin Magajin garin Baltimore da ke Maryland.

Ita ce auta a cikin 'ya'yan iyayenta bakwai.

Ta yi jami'a a Washington inda a nan ne ta hadu da mijinta Paul Pelosi suka yi aure kuma ta sauya sunanta daga Nancy D'Alesandro zuwa Nancy Pelosi.

Sun haifi 'ya'ya biyar - mata hudu namiji daya.

Nancy Pelosi a siyasa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A shekarar 1976 ne ta shiga harkar siyasa, inda ta yi amfani da mutanen da ta sani dalilin iyayenta ta taimaka wa gwamnan jihar California Jerry Brown lashe zaben share-fage a lokacin da ya tsaya takarar shugabancin Amurka.

Nancy ta rike mukamai da dama a jam'iyyar Democrat inda har ta zama shugabar jam'iyyar kafin daga baya a shekarar 1988 ta yi nasarar cin zabe a matsyain 'yar majalisa.

A shekarar 2001, ta tsaya takarar bullaliyar majalisa wato mukami na biyu mafi girma a majalisar kuma ta ci. Da shekara ta zagayo sai ta zama shugabar marasa rinjaye.

Nancy na daya daga cikin manyan 'yan siyasar Amurka da suka soki matakin farmakin da kasarta ta kai Iraqi a shekarar 2003.

Ranar 16 ga watan Nuwambar 2006 ne 'yan majalisar Democrat suka zabi Pelosi a matsayin Kakakin majalisa.

Wannan ya sa ta zama mace ta farko da ta fara rike wannan mukamin a tarihin Amurka.

Ta yi shekara hudu a matsayin kakakin majalisar wakilai kafin 'yan jam'iyyarta ta Democrat ta rasa rinjaye wanda kuma ya yi sanadiyyar saukarta daga matsayin.

Amma a shekarar 2018 ta sake dawowa a matsayin kakaki.

Ta fuskanci kalubale da dama a wannan karon musamman daga 'yan jam'iyyar Republican, wadanda ke ganinta a matsayin mai jawo ce-ce-ku-ce.

Rashin jituwarta da Shugaba Trump

Asalin hoton, AFP

Ana iya cewa takun-saka tsakanin Kakaki Nancy Pelosi da Donald Trump ya bayyana a bainar jama'a ne a lokacin da majalisar da take jagoranta mai rinjayen 'yan Democrat ta ki amincewa da kudirin Trump na gina katanga a iyakar Amurka da Mexico.

Wannan ya haifar da takaddama har aka kai ga rufe wasu ma'aikatun gwamnati tsawon makonni daga karshen 2018 zuwa farkon 2019.

Donald Trump bai taba boye kiyayyar da yake yi wa Pelosi ba inda sau da dama ya kan wallafa sakonnin cin fuska game da ita a shafinsa na Twitter.

Haka zalika, Nancy Pelosi ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen nuna wa Shugaba Trump matsayinta na mace mafi karfin iko da aka zaba zuwa majalisa ta hanyar amfani da salon magana da kafiya a kan abin da 'yan jam'iyyarta suka yarda da shi.

Wani abu da ba za a iya mantawa da shi ba dangane da rikicin Pelosi da Trump shi ne yadda ta yi wa Shugaban tafi bayan da ya gabatar da jawabinsa na shekara-shekara a gaban majalisar dokokin kasar a shekarar 2019 .

A jawabin nasa, shugaba Trump ya yi shagube da habaici wanda mutane da yawa suka fassara su a matsayin sako ga Pelosi. Sai dai maimakon Kakakin ta fusata da kalaman Trump, sai ta shiga tafa masa da karfi har tana miko masa hannuwanta gaba.

Masu sharhi dai sun ga wannan mataki na Pelosi a matsayin raini ko mayar da Shugaba Trump abin tsokana.

Nan da nan aka rika yada bidiyon a shafukan sada zumunta sannan aka kirkiri maudu'in #PelosiClap.

A watan Fabrairun 2020 ne bayan da Shugaba Trump ya gabatar da irin wannan jawabin a gaban majalisa, Pelosi ta yayyaga takardar jawabin nasa.

'Yan jarida sun nadi wannan bidiyo kuma an ta yada shi a shafukan sada zumunta tsawon lokaci.

An zarge ta da cin fuskar Shugaba Trump amma ta kare kanta inda ta ce ta yaga jawabin ne saboda a cike yake da 'karya'.

A iya cewa Nancy Pelosi ta tabbatar da kanta a matsayin mace mai jajircewa kan akidarta, sannan duk da ikon da Shugaba Trump ke da shi ta zamar masa karfen kafa.

Saura kwanaki kadan Trump ya sauka daga mulki, amma Kakaki Pelosi ta yi nasarar sake tsige shi a karo na biyu wanda kwararru ke ganin cewa, ko ba komai tarihi ba zai taba mantawa da Trump a matsayin shugaban da aka tsige sau biyu ba.

Kuma wannan abu ne da ba a taba gani ba tarihin siyasar Amurka.