Bitcoin: Mutumin da zai yi asarar naira biliyan 95 idan ya ɓarar da dama biyu

close up golden bitcoin coin crypto Currency background concept.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mr Thomas ya rubuta lambobin sirrin inda ya adana bitocin ɗin ne a wata takarda, sai ta ɓata daga baya

Wataƙila da yawa daga cikinmu sun taɓa samun kansu cikin halin manta lambobinsu na sirri ta yadda muka gwada sawa sau takwas, ya zame mana saura gwaji biyu kawai a kulle mu.

Wannan halin ne wani mai sarrafa da haɗa manhajoji Stefan Thomas ya samu kansa a ciki, amma nasa yanayin kusan ya fi tsanani don kuwa ya manta lambobin sirrinsa ne na kuɗin intanet ɗin Bitcoin da ke adane a wani ma'ajin bayanan komfuta, wanda darajarsu ta kai dala miliyan 240, kwatankwacin naira biliyan 95.

Jaridar New York Times ta bayyana halin rikicewar da ya samu kansa a ciki, har labarin ya yaɗu tamkar wutar daji.

Wani tsohon shugaban abubuwan da suka shafi tsaro na kamfanin Facebook Alex Stamos yace zai taimaka masa - idan zai ba shi kashi 10 cikin 100 na kuɗin.

Darajar kuɗin Bitcoin ta ƙaru sosai a watannin baya-bayan nan.

Darajar kuɗn Bitcoin ɗaya ya kai dala 34,000, kwatankwacin naira miliyan 13.5.

Sai dai kuɗin intanet ɗn ba shi da tabbas zai iya faɗuwa a kowane lokaci.

Kuma ra'ayin masana ya bambanta kan ko darajarsa za ta ci gaba da hauhawa ko za ta faɗi.

Daloli ƙalilan

An bai wa Mr Thomas, wanda aka haifa a Jamus amma yake zaune a San Francisco, bitcoin 7,002 a matsayin ladan yin wani bidiyo da ya yi inda yake bayanin yadda kuɗin intanet ke aiki fiye da shekara 10 da suka gabata.

A lokacin kuɗin kowane ɗaya bai wuce ƴan daloli ƙalilan ba.

Sai ya adana su a wata manhaja ta ajiya ta intanet IronKey, a cikin ma'ajin bayanan komfuta wato hard drive.

Sannan ya rubuta lambobin sirrin buɗewar a kan wata takarda wacce ta ɓata daga baya.

Bankunanmu

A bisa ƙa'ida za a yi ta ƙoƙarin sanya lambobin sirrin ne sau 10 kawai, idan ba a dace ba daga haka sai a kasa buɗe ma'ajiyar kuɗin.

Ga alama wannan tsaka mai wuya da ya samu kansa ciki ta sanyaya masa gwiwa da harkar kuɗin intanet ɗin.

Ya shaida wa Jaridar New York Times cewa: "Gaba ɗaya basirar cewa kai ne bankin kanka da kanka - kamar yadda nake kiran lamarin, kai ne kake yin takalman da kake sawa?

"Dalilin da ya sa muke da bankuna shi ne ba ma son mu dinga yin duk abubuwan da bankuna ke yi."

Mafita

Mr Stamos, wanda a yanzu farfesa ne a cibiyar sa ido kan harkar intanet ta Stanford Internet Observatory, ya wallafa saƙon Tuwita ga Mr Thomas da ke cewa: "Um, idan kuɗinka na bitcoin da suka kai yawan dala miliyan 220 suka kullu, ba za ka tsaya kana canki canka na gano lambobin sirrinka har sau 10 ba, sai ka miƙa wa ƙwararru lamarin ka sayi lambobin sirri na IronKeys 20 ka shafe wata shida don ƙoƙarin buɗe komai a nutse.

"Zan yi maka hakan idan za ka biya ni kashi 10 cikin 100 na kuɗin.

"Ka kira ni."

Mr Thomas ba shi ne zai zama na farko da ka iya zama miloniya a harkar Bitcoin da damarsu ta kulle ba.

A yanzu haka akwai kusan dala biliyan 140 na kuɗin Bitcoin da suka shiga rububi ko aka rasa su ko aka kasa gano su saboda an manta lambobin sirrin buɗe su, a cewar kamfanin da ke tattara bayanan mu'amalar kuɗin intanet na Chainanalysis.

Kuma kamfanonin da ke taimaka wa a gano kuɗaɗen intanet ɗn na samun buƙatun yin hakan a kowace rana.

Maƙlar New York Times ta kuma bayar vda misalin wani ɗan kasuwa da ya rasa kusan bitcoin 800 a lokacin da wani abokin aikinsa ya goge duk abin da ke kan wata komfuta da ke ɗauke da lambobin sirrin ma'ajiyar kuɗinsa.

Kuma a shekarar 2013 ma, wani mutumin yankin Wales a Ingila ya yashe tulin shara a ƙoƙarinsa na neman ma'ajin bayanan komfuta, hard drive da ya jefar, wanda ke ƙunshe da bitocin 7,500.

A lokacin darajarsu ta kai fam miliyan huɗu, a yanzu kuwa darajarsu za ta wuce dala miliyan 250.