Zaben Nijar: Yadda rantsuwa da AlKur’ani ta jawo ce-ce-ku-ce

Mahamane Ousmane s
Bayanan hoto,

Mahamane Ousmane shi ne shugaban RDR Chanji da zai fafata da dan takarar jam'iyya mai ci ta PNDS Tarayya

Ofishin ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar ya hana 'yan siyasa amfani da Kur'ani yin rantsuwa ba a bisa ka'ida ba.

Da ma dai a zaben da ya gabata na watan Disamba ne aka rika amfani da Al-Kur'anin a wani yunkuri na hana satar kuri'u ko coge.

Ministan harkokin cikin gida ya ce wannan lamari ya saba wa aya ta 8 a kundin tsarin mulkin kasar na 25 ga watan Nuwambar 2010.

Ya ce wannan aya ta raba hukuma da addini domin haka amfani da littafin mai tsarki da suke yi tamkar taka doka ne.

Wannan mataki ya jawo ce-ce-ce-ku-ce a kasar, inda yan bangaren adawa ke ganin cewa tsoro ne ya sa gwamnatin daukar wannan mataki yayin da masu mulki ke ganin matakin ya yi daidai.

Alhaji Duda Rahama na jam'iyyar adawa ta RDR Canji ya ce "son rai ne da tsoro" ya sa gwamnati daukar wannan mataki.

"Idan gwamnati ba ta zargin kanta da komai me ya sa za ta ce kar a yi amfani da Al-Kur'ani? Ko kuma tana zargin kanta da sata ko aringizo shi ya sa take tsoron Al-Kur'ani", a cewarsa.

Ya ce shugabannin da a yanzu suke zaune lafiya sun samu haka ne saboda rantsuwa da suka yi da Al-Kur'ani.

"Da ba su rantse da Al-Kur'ani ba ai da ba za su zauna lafiya ba. Sai muka bar su da Al-Kur'ani da Allah mai Al-Kur'anin, kuma ga su nan," in ji Duda Rahama.

Ya ce domin haka ne su ma yanzu suke sa duk wani wanda suke ganin zai cuce su a yayin zabe yin rantsuwa da laya da Al-Kur'ani.

"Duk wani wanda zai tafka magudin zabe ko ya yi aringizo, ban ga laifi ba don an ce ya yi rantsuwa," a cewar dan siyasar.

Ya kuma soki gwamnati da cewa idan har za a rantsar da shugaban kasa da shugaban kotun koli da sauran jami'an gwamnati da littafai masu tsarki me zai hana 'yan siyasa yin rantsuwa?

Ya ce "Ya zama kenan su ma ba su raba addini da hukuma kenan. Ai duk Al-Kur'ani daya ne".

Ya kuma ce suna sa a daga Al-Kur'anin ne don su tabbatar an yi sahihin zabe.

Amma kakakin jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, Alhaji Usoumanou Mouhammad ya ce rashin sanin madafa ne ke sanyawa a yi irin wannan rantsuwa.

"Wadanda ke kula da zabukan nan wato manyan jami'an CENI sun riga sun rantse da Al-Kur'anin kafin su hau mukamansu, sai ku ma a ce an tsare ma'aikata cikin daji an sa su rantsuwa? Wannan ai ragwanci ne," a cewarsa.

Malam Usoumanou ya ce tsoratar da ma'aikatan zabe kawai a ke so a yi kuma masu sa a yi rantsuwar su ne asalin barayin zaben.

"Wannan ya zama ma suna wasa da Al-Kur'ani da Allah," a cewarsa.

Bayanan hoto,

Ana zargin tursasa wa masu kada kuri'a su rantse da AlKur'ani

Malamai a kasar sun ce wannan matakin sa malaman zabe rantsuwa da littafi mai tsarki bai dace ba.

Malam Haja Alhaji Alolo ya bayyana cewa wannan mataki na iya zama abin cutuwa ga talakawan da ke zuwa kada kuri'a.

"Kur'ani ya fi karfin a yi mai haka. Yin haka kuskure ne babba a shari'a. bai dace a ce wani wanda ba malami ba ya rika yawo da Kur'ani don kawai a ce an sa Kur'ani a wani abu da yake so. Alhali kuma kasar ma akwai wanda ba Musulmi ba" a cewarsa.

Da ma can dai al'adar mutanen Damagaram ce yin amfani da Al-Kur'ani ko laya wadda suke amfani da ita wajen shawo kan matsaloli ko tsakanin mutum da mutum ko gungungu mutane da yin sulhu ya gaza samar da maslaha.

Amma sannu a hankali al'adar ta bazu zuwa sauran sassan Nijar kuma ga shi yanzu lamarin har ya kai ga batun zabe.