Yadda aka sace ƴan kasuwar Kantin Kwari 27 a hanyarsu ta zuwa birnin Aba

A wasu lokutan akan samu mummunan cunkoso a hanyar duk da fama da rashin tsaro
Bayanan hoto,

A wasu lokutan akan samu mummunan cunkoso a hanyar duk da fama da rashin tsaro

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace wasu matasa ƴan Kasuwar Kantin Kwari ta Kano a kan hanyarsu ta zuwa birnin Aba na jihar Abia da ke kudancin Najeriya.

Ƴan bindigar sun tare matasan waɗanda dukkansu ƴan jihar Kano ne, a kan hanyarsu ta zuwa Aba a cikin daren ranar Lahadi.

A cewar ƙungiyar matasan arewacin Najeriya a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, matasan sun tafi garin na Aba a ranar Lahadin da ta gabata don yin sayayya, da niyyar koma wa Kano a makon da muke ciki.

Sai dai ƙungiyar ta ce suna cikin tafiya sai wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne don neman kudin fansa suka harbi tayar motar safa da suke ciki, suka kuma yi awon gaba da su da sauran fasinjojin da ke cikin motar sama da 50.

Sannan kungiyar ta ce ba su sami labarin halin da abokan nasu ke ciki ba sai a ranar Laraba, inda masu garkuwar suka nemi kuɗi kafin su bayar da matasan.

Da farko rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, amma kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Kaduna ya fitar da sanarwa inda ya ce a kan hanyar Kaduna lamarin ya faru ba.

"Hukumomin tsaro na tarayya da ke aiki a kan titin Kaduna-Abuja a wannan lokacin ba su bayar da rahoton faruwar wani lamari kamar haka ba.

"Sannan dukkan binciken da jihar Kaduna ta yi bai gano cewa lamarin ya faru ba a faɗin jihar," a cewar sanarwar.

Shugaban ƙungiyar matasan ƴan kasuwar Arewacin Najeriya da ke Kasuwa Kwari a Kano, Abubakar Babawo ya ce "Sun tafi Aba ne don saro takalma da yaduka amma sai wannan mummunan abu ya faru da su. Aƙalla sun kai 27 kuma yawancinsu masu ƙaramin ƙarfi ne don kuɗaɗensu ba sa wuce naira 300,000.

"Suna ɗan zuwa sare-sarensu ne don samun abin rufin asiri. A cikinsu akwai wanda ba a daɗe da yaye shi ba aka ba shi ɗan jarin da zai dogara da kansa amma sai ga abin da ya faru."

Ya ƙara da cewa mutanen sun tuntuɓi dangin ƴan kasuwar ana ta ciniki. "Amma tuni mun tuntuɓi jami'an tsaro," in ji Abubakar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai ba wai iya wadannan yan kasuwar 'yan bindigar suka ɗauke ba, har da sauran sama da mutum 50 da ke cikin motar safa da ke safara tsakain arewaci da kudancin Najeriya da ke iya ɗaukar kusan mutum 100.

Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin wasu daga cikin makusantan waɗannan matasa da ake zargi ƴan bindiga sun sace, sai dai haƙa ba ta cimma ruwa ba, sakamakon ƙin magana da suka yi, sannan wasu daga cikinsu ma ba su san an ɗauke yaransu ba.

Wannan dai na zuwa ne makwanni kadan bayan da wasu ƴan bindiga suka dauke wani dan kasuwa a garin Minjibir, sannan suka ƙona motar ƴan sanda, amma sai dai bayan biyan kudin fansa sun sako mutumin.

A baya-bayan nan al'ummar Najeriya musamman direbobi da ke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja na kokawa kan yadda masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa suka ddabi hanyar.

Sai dai duk da ikirarin da hukumomin Najeriya ke yi na shawo kan al'amarin, abin na ci gaba da jefa tsoro da faragaba a zukatan al'umma.

Bayanan hoto,

Taswirar titin Abuja zuwa Kaduna