Biden ya kaddamar da shirin tallafin tattalin arziki Amurka na $1.9tn

.

Asalin hoton, Reuters

Zababben Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana wani shirin tallafi na dala tiriliyan 1.9 ga tattalin arzikin da annobar korona ta yi wa illa matuka tun kafin ya kama a iki a mako mai zuwa.

Idan majalisar Amurka ta amince da shirin, shirin zai samar da dala tiriliyan 1 da za a raba wa iyalai, wanda a ciki za a biya kowa ne iyali dala 1,400 kai tsaye ga asusun ajiyar Amurkawa.

Sannan shirin zai samar da dala biliyan 415 da za a yi amfani da shi wajen yaki da annobar korona da kuma dala biliyan 440 da za a yi amfai da su wajen tallafa wa kananan kamfanoni da masana'antu farfadowa.

Mista Biden, wanda dan jam'iyyar Democrat ne, ya yi alkawarin kawo karshen wannan annobar da kawo yanzu ta halaka fiye da mutum 385,000 a Amurka kawai.

A bara ya yi yakin neman zabensa ne kan samar da tattalin arzikin da zai mayar da hankali wajen samar da mafita kan wannan annobar fiye da yadda Shugaba Donald Trump, wanda dan Republican ne ke yi.

Wanann shirin na Mista Biden na zuwa ne a lkacin da ake kara samun karuwar masu kamuwa da cutar yayin da ake kara shiga yanayin sanyi.

A kowace rana, a kan sami fiye da mutum 200,000 da ke kamuwa, ban da ma su mutuwa da yawansu kan zarce 4,000 a kullum.

Me Biden ya ce?

A wani jawabi da ya yi ta talabijin, cikin daren Alhamis daga garinsu na Wilmington a jihar Delaware, ya ce: "Akwai wata babbar matsala da ke wahalar da al'umma a gabanmu kuma babu lokacin da za a bata."

"Lafiyar kasarmu ne ke kan gaba," inji shi, "Tilas mu dauki mataki, kuma tilas mu dauki mataki yanzu."

Shugaban mai jiran gado ya kuma ce: "Lallai za a yi tuntube, amma na yi alkawarin sanar da ku gaskiyar halin da ake ciki kan nasarorin da muke samu da kuma cikas din da za mu ci karo da su."