An samu ƙaruwar cin zarafin mata a Kano

Hukumar Hisbah a Kano ta koka bisa ga yadda ake samun karuwar cin zarafin mata da maza a gidajen aure a Kano.
Hukumar ta ce mafi yawan korafe-korafen da take samu na cin zarafin mata a gidajen miji ne ko kuma na mazaje a hannun matan su.
Shugaban hukumar, Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina, ya ce lamarin na ƙara ta'azzara a 'yan kwanakin nan.
"Al'amarin na da ban tsoro da ban takaici. ƙorafe-ƙorafen da muke samu sun yi yawa. Sai ka ga miji ya doki matarsa da hannunsa har wurin ya tash ya kumbura," a cewarsa.
"Namiji da kansa zai je wajen sirikansa ya nemo auren matarsa amma wai har ya iya daukar hannunsa ya mare ta. Duk muna ganin irin haka ana kawo mana kara a wannan hukumar," in ji Kwamanda Ibn Sina.
Matsalar cin zarafin mata ko maza ko yara kanana matsalace da ke kara ta'azzara a mafi yawancin kasashe.
Mata da dama kan koka bisa ga yadda mazajen su ke cin zarafin su, inda a wasu lokutan har ta kan kai ga mummunan rauni a wasu lokutan ma a rasa rai daga bangarorin biyu.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Sheikh Ibn Sina ya ce duka ba ita ce hanyar horo da ta fi dacewa ba tunda ko a addini ma akwai hanyoyin da aka ware na yi wa mace horo idan ta yi ba daidai ba.
Akasin yadda aka fi gani, a wasu lokutan mata ce ke cin zarafin mijinta ko ma ta yi yunkurin kashe shi kamar yadda a kwanakin baya aka samu wasu matan da ake zargin su da kashe mazajen su ta hanyar caka musu wuka.
A zamanin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, sai da masarautar Kano ta gabatar da wani kudirin doka gaban majalisa, kan yadda za a magance cin zarafin mata, da sauke hakkin iyalai daga bangaren mazajen su.
Sai dai har yanzu ba a kai ga amincewa da kudurin dokar ba.
A watan Yunin bara ne Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an samu karuwar cin zarafin mata a fadin duniya, a daidai lokacin da ake tsaka da kullen annobar korona.
Ana tunanin an samu karin kashi 20 cikin dari a wannan lokaci saboda mutane da yawa na takure a gida da mazajensu ko matansu da ke cin zarafinsu.