Joe Biden ya fara aiki domin sauya dukkan manufofin gwamnatin Trump

US President Joe Biden signs documents after being sworn-in

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Biden bai bata lokaci ba wajen sanya hannu kan dokokin da za su dakatar da alkiblar Amurka kan sauyin yanayi da bambancin launin fata

Shugaban Amurka Joe Biden ya fara kwance dukkan ayyukan mutumin da ya gada Donald Trump, ana sa'o'i kalilan bayan ya sha rantsuwa.

"Babu lokacin da za mu bata kan batutuwan da ke fuskantar mu," kamar yadda ya sanar a wani sakon Twitter yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Fadar White House ji kadan bayan an ransar da shi.

Shugaba Biden ya sanya hannu kan wasu dokokin shugaban kasa 15, ta farkonsu ita ce wadda za ta bunkasa aikin kawar da annobar korona.

Sauran dokokin sun yi watsi ne da manufofin gwamnatin Trump kan sauyin yanayi da shige-da-fice.

Mista Biden ya kama aiki ne a ofishinsa na Oval bayan da aka rantsar da shi ranar Laraba a matsayin shugaban Amurka na 46.

Wannan bikin ya kasance irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Amurka saboda annobar korona, inda aka rage yawan bukukuwa a wanjen rantsar da sabon shugaban.

Donald Trump - wanda har zuwa jiyan bai mika wuya cewa ya sha kaye ba a hannun Joe Biden - ya ki halartar bikin kamar yadda aka saba gani a al'adance.

Waɗanne dokoki Biden ya sanya wa hannu?

Shugaba Biden "zai dauki mataki - ba kawai ta juya wa manufofin Trump baya ba - amma zai yi haka ne domin ciyar da kasarmu gaba," inji wanta sanarwar da aka fitar yayin sanya hannu kan dokokin shugaban kasar.

Akwai wasu jerin matakai da za a dauka domin dakile annobar korona da ta lakume fiye da rayukan mutum 400,000 a Amurka.

Akwai kuma wata bukata ta musamman da za a fitar kan sanya takunkumi da nayar da tazara tsakanin mutane a dukkan gine-gine da ofisoshin gwamnati.

Za a kuma samar da wani sabon ofis da zai rika kawo daidaito kan martanin da Amurka za ta rika mayar wa kan annobar korona - matakin da gwamnatin Trump ta fara aiki a kai - na janyewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Biden na son yi wa Amurkawa miliyan 100 allurar riga-kafi cikin kwana 100 na farkon mulkinsa

Wannan matakin sake kulla dangantaka da WHo ya faranta wa shugaban Majalisar Dinkin Dunya Antonio Guterres, wanda ya ce "abu ne mai matukar muhimmanci" a hada kai wuri guda domin magance annobar korona.

Mista Biden ya kuma dage kan mayar da yaki da sauyin yanayi, wanda zai mayar da shi ciki mayan manufofin gwamnatinsa.

Ya sanya hannu kan mayar da Amurka cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta 2015 wadda aka kulla a birnin Paris, wanda Mista Trump ya janye Amurka daga ciki a bara.

Mista Biden ya kuma kwace wata dama da aka bayar na hakar mai wadda aka fi sani da Keystone XL Pipeline, wanda masu fafutuka ciki har da Indiyan dajin Amurka su ka dade suna kamfen a soke.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Aikin samar da bututun mai na Keystone XL Pipeline ya janyo shekaru na bacin rai

A kan shige-da-fice, Mista Biden ya soke dokar na da Mista Trump ya kafa da ta ba shi damar gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, kuma ya kawo karshen hanin da aka yi wa Musulmi daga wasu kasashe shiga Amurka.

Akwai kuma wasu dokokin da aya sanya wa hannu kan batutuwan nuna bambanci launin fata da daidaito tsakanin jinsunan kasar.