Sunday Igboho: Gobara ta tashi a gidan mutumin da ya umarci Fulani su fice daga Oyo

Ba a san wadanda suka cinna wa gidan wuta ba

Asalin hoton, KOIKIMEDIA

Bayanan hoto,

Mr Igboho ce wasu Yarbawa ne da ke goyon bayan makiyaya suka kona gidansa

Gobara ta tashi a gidan Sunday Igboho, mutumin da ya umarci Fulani makiyaya su fice daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce da misalin karfe uku na asubahin yau Talata wasu mutane suka cinna wuta a gidan Sunday Igboho.

Sai dai ba ya gidan saboda ya tashi daga can inda ya koma wani gidan, amma dai gidan da aka cinna wa wuta shi ne babban gidansa da ke birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet da wasu jaridun Najeriya sun nuna yadda wasu bangarori na gidan suka kone.

Ganau sun shaida wa BBC cewa makwabtan Mr Igboho sun kai dauki a yunkurinsu na kashe gobarar.

Kawo yanzu ba a san wadanda suka tashi wuta a gidan dan bangar kabilar Yarbawan ba.

A ranar Juma'a ne babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarni ga kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo, da ta kamo Mr Sunday Igboho Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a shirin BBC na Ra'ayi Riga.

A cewarsa babban sifeton ƴan sandan ya umarci kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo Mrs Ngozi Onadeko ta kamo Igboho sanna ta kai masa shi Abuja.

Ana zarginsa da jagorantar wani gungun jama'a wajen korar makiyaya daga jihar Oyo.

Sai dai har yanzu ba a kamo shi ba.

A makon jiya Mr Igboho ya je wani kauye mai suna Igangan da ke Ƙaramar Hukumar Ibarapa ta jihar inda ya jaddada cewa dole duka Fulanin da ke zaune a jihar ta Oyo su tashi bisa zargin da ake yi a yankin cewa su ne suke kitsa garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma wasu laifuka da ke faruwa a can.

Martani

Sai dai Mr Igboho, wanda ya je gidan nasa da safiyar na, ya shaida wa manema labarai cewa wasu masu son tayar da hankali ne suka cinna wuta a gidan nasa.

A cewarsa, da misalin karfe uku na asubahi 'yan uwansa da ke gidan suka gaya masa cewa mahara sun je gidan suna harbe-harbe inda suka kuma cinna wa gidan wuta.

Ya ce wasu Yarbawa ne da ke goyon bayan makiyaya suka kona gidansa.

Wane ne Sunday Igboho?

Asalin hoton, SUNDAY IGBOHO

Sunansa na yanke shi ne Sunday Adeniyi Adeyemo amma ana yi masa lakabi da Sunday Igboho.

Rahotanni sun ce ya tashi a yankin Modakeke da ke jihar Osun a kudu maso yammacin Najeriya, amma dan asalin kauyen Igboho da ke jihar Oyo.

Lokacin da yake matashi a Modakeke, Sunday yana sana'ar kanikanci.

Ya soma sharaha ne a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Oyo Rashidi Ladoja saboda goyon bayan da ya nuna masa yayin da ake rigimar tsige gwamnan.

Mr Igboho ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin uban gidansa kodayake ya ce shi ba dan siyasa ba ne.

Cif Igboho yana da mata biyu amma ba tare yake zaune da su a gidansa da ke Ibadan ba.

Wasu rahotanni sun ce daya daga cikin matansa tana zaune a kasar Canada yayin da dayar ke zaune a Jamus.

Wasu rahotanni sun ce shi mutum ne da ke da asiri mai karfi saboda hulda da 'yan tauri.

Wasu daga cikin manyan abokansa taurari ne a fina-finan Yarbawa yayin da wasu kuma mawaka ne.

Karin hotunan gidan Mr Igboho da aka kona