Manoman India: Abin da ya tunzura manoma suka yi ba-ta-kashi da 'yan sanda

Asalin hoton, PTI
Manoman sun karya shingayen da aka gindaya
Manoma sun tsallake shingayen da aka sanya sannan suka jurewa hayaki mai sa kwalla da aka rika fesa musu har sai da suka shiga Delhi babban kasar a ranar hutu ta kasar wadda ake kira India's Republic Day.
Dubban manoma ne suka isa birnin a kan motocin tantan ko tarakta domin yin zanga-zanga a kan sabbin sauye-sauyen da gwamnatin kasar ta yi kan harkokin noman kasar.
A wasu wuraren, manoma sun kakkarya shingayen sannan suka kauce daga kan hanyoyin da 'yan sanda suka amince su bi.
Gangamin da suke yi ranar Talata yana cikin jerin zanga-zanga da suka kwashe wata da watanni suna yi, wadda daya ce daga cikin manya-manyan zanga-zanga da manoma suka yi a tarihin India.
Gwamnati ta yi alkawarin dakatar da sauye-sauyen, sai dai manoman sun ce ba za su daina zanga-zanga ba sai an soke dokar baki dayanta.
Manoma sun kwashe watanni suna zanga-zanga a kan iyakokin birnin Delhi, suna masu masu kira a soke dokar.
'Yan sanda sun amince a gudanar da zanga-zangar ranar Talata bayan sun kwashe tsawon lokaci suna tattaunawa domin amincewa zanga-zangar ba za ta hana faretin ranar Republic Day ba.
Ana sa ran masu zanga-zangar za su ci gaba da shiga birnin Delhi daga bangarori shida da ake shiga sai dai 'yan sanda sun sanya shingaye a dukkan wuraren inda suka umarci manoman su yi amfani da wasu hanyoyi da aka ba su dama.
Cikinsu har da hanyoyin da ke wajen birnin.
Sai dai kungiyoyin manoman sun taru a kan iyakoki irin su- Singhu, Tikri da Gazipur - inda suka balla dukkan shingayen sanna suka shiga birnin a kafa da kuma cikin tantan.
Asalin hoton, PTI
'Yan sanda sun fesa hayaki mai sa kwalla kan wasu masu zanga-zangar domin su tarwatsa su
Wani manomi a kusa da kan iyakar Ghazipur ya shaida wa BBC "Tabbas sai Mr Modi ya janye wadannan bakaken dokoki." Ya kara da cewa duka manoman sun bar kan iyakar sun nufi tsakiyar birnin Delhi.
Akwai yiwuwar barkewar rikici bayan da aka haramta musu shiga cikin birnin Delhi inda ake gudanar da tarukan bukukuwan na hukuma.
Manoman sun ce za su tunkari majalisar dokoki
Bikin faretin ya kunshi nuna sabon samfurin kayayyaki da motocin yakin da sojoji za su yi da kuma yi nunin al'adun gargajiya daga jihohi daban-daban a dandalin.
Faretin wannan shekarar takaitacce ne, kuma babu hayaniya sosai saboda annobar korona.
Dokoki da suka jibanci kayyade wa manoma farashin amfanin gona daga manyan kamfanoni, sun haifar da zanga-zanga a lokacin da mutane suka kutsa cikin ginin majalisar dokoki a cikin watan Satumbar da ya gabata.
Asalin hoton, Getty Images
Manoman sun ce dole gwamnati ta soke dokokin da ta sauya kan noma
Asalin hoton, Getty Images
Manoman sun kwashe kwanaki da dama suna isa kan iyaka a kan tantan
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Bayan da Firaiminista Narendra Modi da jam'iyarsa BJP ta goyi bayan gyare-gyaren, kungiyoyin manoma sun yi wa hakan lakabi da ''mutuwar tsaye'' da hakan zai saka su cikin barazana daga kamfanonin.
Zanga-zangar ta cigaba da gudana, yayin da dubban manoma daga jihohin arewaacin Punjab Haryana suka yi tattaki zuwa birnin Delhi a karshen watan Nuwamba suka fara zaman dirshan a kan iyakar, wanda da dama har yanzu suna kan gudanarwa.
Mene ne takamaimen abubuwan dokokin suka kunsa?
Gabaki daya, dokokin sun shimfina ka'idoji a bangaren sayarwa da saka farashi da kuma adana amfanin gona - ka'idojin da suka saba kare muradan manoman kasar India daga dadadden tsarin kasuwanci na kara-zube.
Daya daga cikin manyan sauye-sauye shi ne za a amince wa manoman su sayar da amfanin gonarsu kai tsaye ga 'yan kasuwa masu zaman kansu - kamfanoni masu sarrafa amnafin gona da manyan shaguna sayar da kayan masarufi da kuma masu sayar da kayan abinci ta yanar gizo.
Fiye da kasha 90 bisa dari na manoman kasar India suna sayar da amfanin gonarsu ne a kasuwa - kuma kashi 6 bisa dari a cikinsu ne kawai ke samun tabbataccen farashin amfanin nasu da gwamnati ta bayar da tabbaci a kai da ake kira 'mandis'.
Asalin hoton, Getty Images
Amma galibi manoman sun fi damuwa kan cewa hakan daga bisani zai haddasa kawo karshen kayyadajjen farashin kasuwa na gwamnati da tsayayyen farashin, wanda za su kasance ba su da wani zabi na shirin ko-ta-kwana.
Hakan na nufin idan ba su gamsu da farashin da masu saye suka nema ba, ba za su iya dawowa kan tsarin na gwamnatin ba ko kuma su yi amfani da shi wajen tattaunawa kan tayin farashin.
Akasarin manoman masu zanga-zangar sun fito ne daga jihohin Punjab da Haryana, inda muhimman amfanin gonar da ake nomawa kamar su alkama, da shinkafa ake sayar da su a tsarin mandi na tsayayye kuma tabbataccen farashi na 'mandis'.
Shin ana bukatar wadannan sauye-sauye?
Akasarin masana harkokin tattalin arziki da kwararru sun amince cewa bangaren ayyukan gona na India na bukatar garanbawul.
Amma masu sukar lamirin gwamnati sun ce ta gaza wajen bin tsarin tuntuba kuma bata dauki kungiyoyin manoma da muhimmanci ba kafin ta zartar da wannan doka.
Abin da ya faru, an gabatar da kudirin dokar cikin gaggawa a majalisar dokoki, ba tare da bayar da isasshen lokacin tafka muhawara ba, wanda ya fusata bangaren 'yan adawa.
Kana gwamnatocin jihohi, da ke taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da irin wannan doka su ma an ajiye su a gefe daya.
Asalin hoton, Getty Images
Daruruwan mata sun shiga zanga-zangar goyon bayan manoman
Kwararru sun kuma yi nuni da cewa sauye-sauyen sun gaza yin la'akari da cewa har yanzu bangaren ayyukan noma shi ne babban jigo a tattalin arzikin India.
Fiye da rabin al'ummar kasar India na aikin noma ne, amma bangaren da kyar yake samar da kasha shida na irin kayyakin da kasar ke samarwa.
Koma baya wajen samar da amfanin gona da rashin cigaban zamani ya rugurguza hanyar samun kudin shiga da kuma haifar da tafiyar hawainiya a harkar noma cikin shekaru da dama.
Yanzu haka, gwamnati ta samar wa da manoma da sauki, ta dauke musu biyan haraji da inshorar amfanin gona, ta kuma bayar da tabbacin mafi kankantar farashin amfanin gona 23 da kuma yawan yafe musu basassuka.
"Yanzu gwamnati na cewa, za mu yi duk abinda za mu yi, kana ta bukace mu da mu yi kasuwanci kai tsaye da manyan kamfanoni. Amma tun farko ma mu bamu bukaci hakan ba! Don haka me yasa suke yi mana hakan?'' Rakesh Vyas, wani manomi ya shaida wa BBC.
Kwararru sun ce duk wani yunkuri na barin tsohon tsarin da aka saba shekara da shekaru zai samu nasara ne ta hanyar zaman tattaunawa, saboda fargaba da kuma zargi ka iya haifar da cikas game da wannan tsarin sauye-sauye.