Harriet Tubman: Tarihin bakar-fatar da Joe Biden zai sanya hotonta a takardar kuɗin $20

Asalin hoton, Getty Images
Harriet Tubman ta zama 'yar leken asiri da kuma ma'aikaciyar jinya a lokacin Yakin Basasa
Gwamnatin Biden ta ce za ta ƙarfafa shirin sanya hoton ƴar fafutukar nan da ta yi gwagwarmayar yaƙi da bautarwa, Harriet Tubman a takardar kuɗin ƙasar na dala 20.
Tun a shekara ta 2020 aka yi tunanin za a aiwatar da wannan shiri, na sanya hoton Ms Tubman da aka haifa a matsayin baiwa a 1820 a takardar kuɗin.
Ma'aikatar baitul-malin ƙasar ta ce hoton Tubman zai maye gurbin tsohon shugaba, Andrew Jackson, wanda ya mallaki bayi.
Sai dai wannan yunƙuri ya fuskanci tsaiko ƙarƙashin mulkin tsohon shugaba Donald Trump, wanda ya sanya siyasa a cikin batun.
Yanzu shugaba Biden ya sake farfado da shirin, kamar yadda mai magana da yawun fadar White House, Jes Psaki ta shaidawa manema labarai.
Jen ta ce nan ba da jimawa ba za a aiwatar da wannan canji.
Idan hakan ya tabbata, Ms Tubman za ta kasance bakar-fata ƴar Afirka da za a buga hoton ta a jikin takardar kuɗi na dala 20, kuma mace ta farko a tarihi Amurka da ke samun wannan matsayi a cikin sama da shekaru 100.
"Yana da muhimmanci a kudinmu su kasance dauke da tarihin kasarmu da kuma yadda take karbar kowa da kowa, kuma sanya hoton Harriet Tubman a takardar $20 zai nuna hakant," a cewar Ms Psaki ranar Litinin.
Takardar kudin $20 ta gwaji mai dauke da hoton Tubman
Matan da a baya aka sanya a takardun kudin Amurka sun hada da Martha Washington, mai dakin tsohon shugaban kasa wadda aka sanya a takardar kudin $1 tsakanin 1891 zuwa 1896, da hoton rukunin mata 'yan asalin Amurka da aak sanya a $20 daga 1865 zuwa 1869.
Amma ba da wuri ake sa ran fitar da takardar kudin ba saboda da sarkakiyar da ake fuskanta wajen tsarawa da kuma samar da takardun kudin Amurka.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
A shekarar 2019, Sakataren Baitul-Mali a lokacin Mr Trump, Steven Mnuchin, ya ce za a jinkirta kera kudin zuwa akalla 2026. A lokacin, ya ce ya mayar da hankali wajen sake tsara takardun kodun ta yadda masu kera kudin jabu ba za su iya yin hakan ba, ba wai sauya hotunan da ke jikinsu ba.
Mr Trump, wanda Andrew Jackson, mutumin da ya yi cinikin bayi yake matukar birgewa, ya bayyana adawarsa da sake fasalin kudin.
Sai dai a lokacin da yake yakin neman zabe a 2016, Mr Trump ya nuna cewa zai sanya hoton Ms Tubman a takardar kudin $2.
Wace ce Harriet Tubman?
An haifi Ms Tubman a matsayin baiwa a 1820, kuma ta girma tana aiki a gonar auduga da ke yankin Dorchester a Maryland. Ita ce 'ya ta hudu a cikin 'ya'yan iyayenta tara. Iyayen nata, Benjamin Ross da Harriet Rit, bayi ne.
Lokacin da take yarinya, wani mai lura da bayi ya kwada mata rodi a kanta lamarin da ya sanya ta ji rauni mai tsanani.
Ta tsere daga gonar da bayi suke aiki a 1849, inda ta tafi Pennsylvania.
Asalin hoton, Reuters
Shekaru da dama bayan haka, Ms Tubman ta koma Maryland sau da dama inda ta ceto mutanen da ke kangin bauta.
An yi kiyasin cewa ta koma Maryland sau 13 inda ta ceto bayi fiye da 70, cikinsu har da 'yan uwa da kawayenta.
Daga bisani ta zama 'yar leken asiri ta sojojin Amurka a lokacin Yakin Basasa, fitacciyar mai fafutukar ganin an bai wa mata 'yancin yin zabe da kuma shahararriyar mai fafutukar ganin an kawo karshen cinikin bayi.
Bayan kammala yaki, Ms Tubman ta tafi jihohin gabashin kasar inda ta rika jawabi kan fafutukar ganin an bai wa mata 'yancin kada kuri'a.
Ta mutu a 1913, tana da shekara 91, zagaye da 'ya'ya da 'yan uwanta.