Buhari ya sauke Buratai da sauran manyan hafsoshin sojin Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Government
Janar I. Attahiru shi ne sabon babban hafsan sojan ƙasa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasar tare da yi masu ritaya.
Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adeshina ya fitar ta ce shugaban ya maye gurbinsu da sabbin manyan hafsoshin sojin.
Hafsoshin sojin sun ƙunshi babban hafsan tsaron ƙasar Janar Abayomi Olonisakin; da babban hafsan sojin ƙasa Janar Tukur Buratai; da babban hafsan sojin sojan ruwa Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar.
Shugaba Buhari ya nada su kan mukaman ne a shekarar 2015 bayan ya yi nasara a zabe karon farko.
Shugaban ya naɗa sabbin manyan hafsoshin sojin kamar haka:
Janar Leo Irabor - shi ne aka naɗa babban hafsan tsaro
Janar I. Attahiru - babban hafsan sojan ƙasa.
Rear Admiral A.Z Gambo - babban hafsan sojan ruwa
Air-Vice Marshal I.O Amao - babban hafsan sojan sama.
A sanarwar, Shugaba Buhari ya gode wa hafsoshin sojin masu barin gado waɗanda ya ce "sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarinsu na samar da zaman lafiya a ƙasa tare da yi masu fatan alheri."
Shin ba a makara ba?
Asalin hoton, Getty Images
Galibin 'yan Najeriya sun dade suna kokawa kan gazawar manyan hafsoshin sojin da aka kora daga aiki
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
'Yan Najariya da dama ciki har da majalisun tarayyar ƙasar sun yi ta kiraye-kirayen a aiwatar da sauye-sauye cikin harkokin tsaron Najeriya.
Kuma kiraye-kirayen sun fi karkata ga buƙatar sallamar manyan hafsoshin tsaro saboda yadda ake fuskantar ƙaruwar ƙalubalen tsaro a ƙasar.
Cikin sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar ba ta fadi dalilin sauke hafsoshin sojin ba, amma ga ƴan Najeriya ba ya rasa nasaba da matsin lamba da kuma gazawarsu, wani abu da za su iya cewa an makara.
Matsalar ƴan fashi masu garkuwa da mutane da satar shanu sai ƙara girma take a yankin arewa maso yammaci baya ga kuma girman barazanar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Magance matsalar tsaro na cikin manyan alkawulan da Shugaba Buhari ya yi wa ƴan Najeriya a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2015.
A saƙonsa na kirsimetin 2020, shugaba Buhari ya ce matsalolin tsaron da ƙasar ke fama da su, sun fi ƙarfin 'yan shawarwarin da ake bazawa a gari a matsayin hanyoyin shawo kansu.
Sai dai duk da hukumomi na cewa an samu nasararori a yaƙi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas da kuma kakkabe ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane domin kudin fansa, har yanzu ana kai hare-hare a yankunan.