Zaɓen 2023: Abin da ya sa wasu gwamnonin APC ke son jam'iyyar ta tsayar da Jonathan takara a 2023

Jonathan da wasu jagororin jam'iyyar APC yayin da suka kai masa ziyara a kwanakin baya

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Jonathan da wasu jagororin jam'iyyar APC yayin da suka kai masa ziyara a kwanakin baya

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan rahotannin da ke cewa jam`iyyar APC mai mulki na zawarcin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan domin ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a karkashin tutart jam'iyyar a zaɓen 2023.

An ce wasu gwamononi daga arewacin kasar ne ke matsawa wajen ganin hakan ta tabbata, inda suka bayar da hujjar cewa saboda wa`adi ɗaya kawai tsohon shugaban ƙasar zai yi, sai mulki ya sake komawa yankin arewacin ƙasar.

To amma masana game da siyasar ƙasar na cewa hakan alama ce da ke nuna rashin aƙida a tsakanin ƴan siyasa masanman ƴan jam'iyyar ta APC mai mulki.

A cewar masanan, wasu manyan jam`iyyar sun gwammace tsohon shugaban ƙasar ya kasance magajin shugaba Buhari, saboda ba zai musu bi-ta-dakulli ba, bayan haka ma zai fi daɗin tafiya a kan wanda zai fito daga wata shiyya ta daban, ko daga shiyyar kudu maso yammaci ko kudu maso gabashin kasar, sannan kuma ba zai wuce wa`adi daya ba,kuma bayan hakan sai mulki ya dawo ga 'yan arewa ganin cewa tun a baya ya yi wa'adi guda.

Dr Abubakar Kari, malami ne a jami`ar babban birnin tarraya na Abuja ya furta cewa ''Wannan na nuna cewa a siyasar Najeriya babu aƙida babu alƙibila, kuma komi ya na iya faruwa.

Asalin hoton, FEMIADESINA

Bayanan hoto,

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Jonathan da shugaba mai ci Muhammadu Buhari

A cewarsa, ''Idan kuma ba haka ba Goodluck Jonathan wanda a baya aka taru baki daya aka ce ya gaza ,ya kasa , mulkin sa ya yi rauni kwarai da gaske kuma a ce shi ne yanzu za a ruka zauwarcin sa ya dawo ya sake mulkin kasar''.

Sai dai masanin ya kara nanata cewa: ''Irin wannan komen ba alheri ba ne ga ƙasa kamar Najeriya.''

Zuwa yanzu dai, babu wani bayani daga jam`iyyar APC mai mulki da aka ce ta na neman zawarcin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan don ya mata takara a zaɓe mai zuwa na 2023.

Bugu da ƙari har daga bangaren tsohon shugaban ƙasar babu wani da ya fito ya ɗaga yatsa domin musunta wannan maganar.

To amma ta wani ɓangare wasu ƴaƴan jam`iyyar ta APC na cewa rungumar tsohon shugaban kasar babban kuskure ne!

Asalin hoton, AFP

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Alhaji Ibrahim Masari, jigo ne a jam'iyyar ta APC mai mulki na cewa:' ''Yin haka ya kasance tamkar renawa talakan Najeriya hankali da wayo ne, mutumin da jam'iyyar APC ta yi wa zarge -zarge masu yawa bila-adda-din, bayan shekaru takwas a ce ya dawo ya yi takara ƙarƙashin wannan jam'iyar, wannan na nufin cewa dukan mu ƴaƴan jam'iyar APC da magoya bayanta sun yi karya? ko kuma sake rikiɗa ya yi ?''

A watan Nuwamban bara ma, an yi ta ka-ce-na-ce bayan wata ziyarar taya murnar zagayowar ranar haihuwa, da shugabannin APC suka kai wa tsohon shugaban ƙasar a jiharsa ta Bayelsa, wadda a baya ba a san jam`iyyar da wannan al`adar ba, kodayake kakakinta ya ce ziyara ce ta zumunci da ba siyasa a ciki.

Duk da cewa da wai-wai ake maganar takarar tsohon shugaba Jonathan a APC a zaɓe mai zuwa na 2023, masana na cewa manuniya ce ga irin gwa-gwa-gwar da za a yi a jam`iyyar nan da zaben 2023, ganin cewa akwai wasu manya da suka bauta wa jam`iyyar, irin su Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni, waɗanda tuni wasu ƴan jam`iyyar suka fara tallata su, ko m dai ake ciki 'yar manuniya za ta nuna kuma ta tabbatar da gaskiyar lamarin.