Cutar Korona : Afrika ta kudu ta sassauta dokar kulle

Asalin hoton, AFP
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sassauta wasu dokoki masu tsauri da aka sanya, yayin da ake samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar korona a kasar.
A wani jawabi da shugaban kasar ya yi ta gidan talabijin din kasar ya ce an sassauta dokokin ne saboda a halin yanzu yawan masu kamuwa da cutar a Afirka ta Kudu ya yi ƙasa sosai saɓanin yadda aka saba gani tun Disamban bara.
Ya ce kodayake har yanzu ana samun masu kamuwa da cutar, lokaci ya yi da za a daidaita dokokin da ake da su.
A halin yanzu wuraren yin taron addini da na sayar da barasa na iya komawa harkokinsu daga ranar Litinin zuwa Alhamis.
Sannan an rage lokacin takaita zirga-zirga, inda daga yanzu dokar za ta koma aiki daga karfe 11 na dare zuwa 4 na Asubahin kowacce rana.
A ranar da alluran rigakafin farko suka isa Afirka ta Kudu, shugaba Ramaphosa ya ce ma'aikatan kula da lafiya ne za su fara karbarta.
Ya ce babu wanda za a tilastawa yin rigakafin, ko kuma a hukunta shi saboda bai yi ba, amma ya jaddada cewa an tabbatar da tana da inganci.