#OccupyLekkiTollGate: Yadda yunƙurin sake buɗe toll gate ɗin Lekki ya jawo ce-ce-ku-ce

Asalin hoton, Getty Images
Toll Gate ɗin Lekki
Ƴan Najeriya sun fara wani gangami mai taken #OccupyLekkiTollGate a shafin Tuwita bayan da aka sanar da sake bude toll gate din unguwar Lekki ta jihar Legas.
Kwamitin jin bahasi da gwamnatin jihar Legas din ta kafa kan harbe-harben da wasu ƴan ƙasar suka ce sojoji sun yi wa masu zanga-zanga ranar 20 ga watan Oktobar 2020 ne ya amince da sake buɗe toll gate din.
Da ma dai tun da lamarin ya faru aka rufe karɓar kuɗi a toll gate din amma masu mota da babur na wucewa salin alin.
Rundunar sojojin Najeriya da gwamnatin tarayya da gwamantin jihar Legas duk sun musanta cewa sojoji sun buɗe wa masu zanga-zanga wuta a Lekki.
Masu zanga-zangar kuma sun kafe a kan cewa sojoji sun buɗe wuta kuma sun kashe mutane da dama - asali ma sun yi ta yaɗa wasu hotuna ɗauke da hotunan mutane da raunuka a jikinsu domin isar da sakonsu.
Wannan ya janyo sabon rikici a wasu sassan Najeriya kuma wasu ɓata-gari sun yi amfani da wannan damar wajen fasa shaguna da sace-sace da lalata masana'antu har ma da kisan ƴan sanda.
Bayan haka ne gwamnatin jihar Legas ta kafa kwamitin mai mutum 9 domin bin diddigin ainihin abin da ya faru a ranar.
Kuma a yanzu mutum biyar cikin 9 na kwamitin sun amince a bai wa kamfanin Lagos Concession Comapny damar buɗe toll gate ɗin na Lekki yayin da mutum 4 suka ce ba su amince ba.
Ce-ce-ku-ce a shafin Tuwita
Nan da nan masu amfani da shafin Twitter, inda nan ne aka fi yayata zanga-zangar ko a bara ma, suka ƙirƙiri sabon maudu'i da ke nuna cewa za su yi sabuwar zanga-zanga a toll gate ɗin na Lekki ranar Asabar, 13 ga Fabrairun 2021.
Waɗannan matasa dai na ganin cewa ba a yi wa waɗanda suka ce an kashe a wurin adalci ba idan har aka sake buɗe shi ba tare da wani takamaiman bayani kan hukunci da za a yi kan sojojin Najeriya ba.
Sannan wasu na ganin cewa da ma kwamitin bahasin na bogi ne, gwamnati ba ta kafa shi da niyyar samun sahihan bayanai ba sai don ta kwantar da hankalin matasan masu zanga-zangar.
Matasan na aika saƙonni mai ɗauke da bayanan abubuwan da ya kamata a yi a safiyar 13 ga watan Fabrairu da suka shirya gudanar da zanga-zangar.
Wani mai amfani da shafin Tuwita Sun ya ce "bayan kun harbe 'yan uwana a lokacin da kuka yi mana kisan kiyashi a Lekki, yanzu kuma za ku sake buɗe toll gate ɗin ku riƙa karɓar kuɗi? Lallai kanku ya kwance!"
Ita ma wata mai suna Hauwa L a shafin na Tuwita ta bayyana ɓacin ranta kan batun sake buɗe toll gate ɗin Lekki.
"Ba a warware abin da ya faru ranar 20 ga watan Oktoba 2020 ba amma shi ne za ku bude Lekki toll gate, macuta," kamar yadda ta wallafa.
Asalin hoton, TWITTER/DINI
Ana yaɗa hotuna masu ɗauke da bayanan yadda za a gudanar da zanga-zangar da lokacin da za a gudanar da ita
Haka kuma, baya ga saƙonni da ake ta wallafawa, wasu na wallafa hotuna dauke da bayanan yadda zanga-zangar za ta kasance.
Sai dai akwai ƴan Najeriyar da ba su amince da wannan shiri ba.
Wasu na ganin cewa wani salon tada husuma ne da neman magana daga wasu ƴan tsiararun matasa a ƙasar masu kiran kansu matasan "soro soke" wanda ke nufin "masu ɗaga murya".
Wannan mai amfani da Twitter ya gargaɗi masu hanzarin cewa za su shiga zanga-zangar ne.
Ya ce "Mafi yawa masu yaɗa maudu'in #OccupyLekkiTollGate na yi ne kawai don kuɗin da suke sa rai za su shigo hannunsu dalilin zanga-zangar. Ku kula."
Yayin da matasa ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate a shafukan sada zumunta, gwamnati ba ta ce uffan ba kan wanann lamari.
Masu shirya zanga-zangar sun ce ba za su amince a buɗe toll gate ba har sai gwamnati ta fitar da sakamakon binciken da kwamitin jin bahasi kan harbe-harben da aka yi a ranar 20 ga watan Oktoba.
Haka kuma, sai an yanke hukuncin da ya dace. Wasu ma na cewa sai rundunar sojin Najeriya ta amince kuma ta dauki alhakin kashe wasu masu zanga-zangar a Lekki.
Sannan, gwamnati ta biyya diyya ga iyalan dukkan waɗanda ƴan sanda a faɗin ƙasar suka kashe ba a bisa ƙa'ida ba. Dama dai wannan ne musabbabin zanga-zangar #EndSARS tun farko.
Don haka a shirye suke su yi zaman dirshan iya tsawon lokaci da za su samu maslaha da gwamnati.
Asalin hoton, Getty Images
DJ Switch na daya daga cikin matasan da suka yi ruwa suka yi tsaki a lokacin zanga-zangar £EndSARS