Riga-kafin Covid-19: Kamfanin BUA ya sayi alluran AstraZeneca miliyan ɗaya

BUA na sa ran sayen alluran riga-kafi miliyan biyar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

BUA na sa ran sayen alluran riga-kafi na AstraZeneca miliyan biyar

Kamfanin BUA mallakin hamshakin dan kasuwar nan na Najeriya Abdussamad Isyaka Rabi'u ya sayi alluran riga-kafin korona miliyan daya domin raba wa 'yan kasar a kyauta.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Litinin ta ce ya sayi alluran riga-kafi na kamfanin AstraZeneca kuma a makon gobe za a kai su Najeriya.

BUA ya sayi alluran riga-kafin ne ta hannun shirin samar da riga-kafi mai suna AFREXIM Vaccine programme tare da hadin gwiwar kwamitin shugaban Najeriya da ke yaki da cutar korona.

"Za a kai alluran riga-kafin makon gobe, kuma za su kasance riga-kafi na farko da za a kai Najeriya tun da aka samu riga-kafin COVID-19. Kazalika za a raba wa 'yan Najeriya alluran riga-kafin a kyauta," a cewar BUA.

Shugaban BUA Abdul Samad Rabiu ya ce: "Baya ga wannan, BUA ya sha alwashin sayen alluran riga-kafi miliyan biyar da zarar sun samu ta hanyar da aka tsara."

Ya ce za a mayar da hankali wajen yi wa ma'aikatan lafiya allurar kafin daga bisani a yi wa kowanne dan kasar.

Ya mika godiyarsa ga shugaban Afrexim Bank, Dr. Benedict Oramah bisa yadda ya tabbatar da sayen alluran riga-kafin da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele, bisa hada gwiwa da kwamitin shugaban kasa da ke yaki da korona wajen ganin an sayi alluran riga-kafin.

Ya zuwa ranar Lahadi, mutum 139,748 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya jimilla, yayin da kuma aka sallami mutum 113,525 sai kuma mutum 1,667 da suka mutu, bisa alkaluman hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar, NCDC.