Boko Haram: Yadda al'ummar Shuwa Arab daga Borno ta kafa sabon gari a Bauchi

Boko Haram: Yadda al'ummar Shuwa Arab daga Borno ta kafa sabon gari a Bauchi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Kimanin mutum miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, musamman ma dai jihar Bornon.

Daga cikin mutanen da rikicin ya shafa akwai wata jama'ar Shuwa Arab da suka kasa zaman sansanonin gudun 'yan gudun hijira, maimakon haka suka nemi wani wajen da za su zauna su ci gaba da rayuwa cikin walwala.