Ngozi Okonjo-Iweala: Tsohuwar ministar kuɗin Najeriya ta zama shugabar WTO
- Daga Kunle Falayi
- BBC News, Lagos

Asalin hoton, Reuters
Kasancewar ta tsallake daga dambarwar siyasa a Najeriya, inda aka sace mahaifiyarta matsayin wata barazana, kuma zama ta a Bankin Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala bai kamata ta sami matsala a mu'amalarta da masu ruwa da tsaki a sabon aikinta na shugaban Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO).
Mai shekara 66 da haihuwa za ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar.
Duk da kwanan nan da samu karɓi takardar zama ƴar ƙasar Amurka, tana alfahari da kasancewarta ƴar Najeriya kuma tana da kishin ƙasa - tana nuna asalinta na Afirka ta hanyar tufafin da suka dace da Afirka.
Ta taɓa faɗa wa BBC a 2012 cewa ta rungumi irin tufafinta a matsayin uwar yaƴa huɗu ma'aikaciya, ta ƙiyasta tufafin da take saka wa na atamfa kowanne ya kai kimanin dala $ 25.
Masaniyar tattalin arzikin da ta ya yi karatu a Jami'ar Harvard a matsayin mai kwazo da jajircewa, kamar yadda ta faɗa wa BBC HardTalk a watan Yuli cewa abin da WTO ke bukata shi wanda zai tabbatar da sauyi.
"Suna buƙatar wani abu sabo, ba zai iya zama kasuwanci kamar yadda aka saba a kungiyar WTO ba - [suna buƙatar] wani da ke son kawo sauye-sauye da jagoranci."
Sauyi a Najeriya
A cikin shekaru 25 da ta yi a Bankin Duniya, an yaba mata ga wasu tsare-tsare don taimakawa kasashe masu karamin ƙarfi, musamman tara kusan dala biliyan 50 a shekarar 2010 daga masu ba da tallafi ga Kungiyar Ci Gaban Kasa da Kasa (IDA), gidauniyar Bankin Duniya ga kasashe matalauta.
Amma sauyin da ta kawo a Najeriya shi ne take alfahari da shi - musamman kasancewar sau biyu da ta riƙe matsayin ministar kudin ƙasar a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Asalin hoton, Getty Images
Okonjo-Iweala ta bar aikin da ake biyanta albashi sosai a Bankin Duniya kuma ta bar iyalinta a Washington ta zama minista a Najeriya
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da ta samu shi ne jagorantar wata tawaga da ta tattauna kan bashin dala biliyan 18 a shekarar 2005 kan kasar, wanda ya taimakawa aka yaba wa Najeriya a karon farko kan rage bashin da ke kanta.
Bashin da ake bin ƙasar tun a farkon shekarun 1980, kuma ya ci gaba da ƙaruwa har dala biliyan 35 saboda ruwa da jinkiri biya har wajejen 1990.
Sauye-sauyen tattalin arzikinta sun yi tasiri sosai kuma sun taimakawa Najeriya a cikin wani mawuyacin lokaci, a cewar fitaccen masanin tattalin arzikin Najeriya, Bismarck Rewane.
Wannan ya haɗa da cire kasafin kuɗin ƙasar daga farashin mai, wanda hakan ya ba Najeriya damar ajiyar kuɗi a wani asusu na musamman a lokacin da farashin mai ya yi tsaɗa.
"Wannan ne ya taimaka tattalin arzikin Najeriya ya farfaɗo tsakanin 2008 da 2009," kamar yadda Mista Rewane ya shaida wa BBC.
Okonjo-Iweala ta bar aikin da ake biyanta albashi sosai a Bankin Duniya kuma ta bar iyalinta a Washington, inda mijinta ke aiki a matsayin likita, ta dawo ta karɓi aiki a Najeriya, inda ba kamar sauran ministocin ba, ba ta da ma'aikata da ke hidimar gida ko tara motoci.
Ta ma fi son ta yi girki da kanta a lokacin da za ta iya, da farfesun bindin shanu a matsayin wanda ta fi so, kamar yadda ta bayyana a hirar jaridar Financial Times ta yi da ita a shekarar 2015.
Ba sani ba sabo
Sauye-sauyen da ta kawo da kuma musamman yadda ta yaƙi cin hanci da rashawa a bangaren mai, inda wasu ƴan kasuwa da ake kira marketers - suka yi iƙirarin a biya su maƙudan kuɗaɗe na tallafi daga gwamnati ga man da ba su sayar ba.
Mahaifiyarta, Kamene Okonjo - likita ce kuma farfesa a fannin ilimin zamantakewar al'umma - an taɓa yin garkuwa da ita a gidanta a kudancin Najeriya a shekarar 2012, tana da shekara 82.
Satar mutane domin kuɗin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya, inda ake samun kudi mai tsoka kuma mutane suna biya tun da jami'an tsaro ba su cika kuɓutar da waɗanda aka sace ba.
Ministar kudi ta wancan lokacin ta ce masu garkuwar sun fara neman ta yi murabus sannan kuma suka nemi a ba su kuɗi.
'Don't leave Africa behind in coronavirus battle'
Amma ta ce ta bijerewa buƙatunsu,
Tarihinta
- An haife ta a 1954 a Najeriya
- Ta yi karatu a Jami'ar Harvard a 1973 zuwa 76 ta yi digiri na uku a cbiyar fasaha ta Massachusetts Institute of Technology (MIT) a 1981
- Ta shafe shekara 25 a Bankin Duniya, har ta kai matsayin ta biyumafi girma tsakanin 2007 zuwa 2011
- Sau biyu tana riƙe muƙamin ministar kuɗi 2003 zuwa 2006 da kuma 2011 zuwa 2015 - Mace ta farko da ta taɓa riƙe muƙamin
- Ta taɓa riƙe muƙamin ministar harakokin waje 2006,kuma mace ta farko da ta taɓa riƙe muƙamin
- Mamba ce kwamitin gudanarwar da Bankin Standard Chartered da kuma Ƙawancen duniya kan rigakafi (GAVI)
- Buhari ya zaɓe ta a matsayin shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya WTO a watan Yunin 2020.
'Zan iya jure wa wahala'
Watakila ta samu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukanta ne saboda yadda ta fuskanci tsantsar talauci. Ta zauna tare da kakarta har sai da ta kai shekara tara a duniya saboda iyayenta suna kasashen waje inda suke karatu.
Ta shaida wa BBC a 2012 cewa: "Sun kwashe kusan shekara goma kafin na sanya su a idanuna ko kuma na sansu. Na yi dukkan abin da yarinyar ƙauye take yi, na riƙa ɗebo ruwa, da zuwa gona tare da kakata da kuma yin ayyukan gida. Na ga tsantsar talauci da abin da yake nufi."
Abubuwan da ta gani lokacin yaƙin basasa na Biafra tsakanin 1967-1970 ya tabbatar da hakan.
Iyayenta 'yan kabilar Igbo sun yi asarar dukkan abin da suka mallaka lokacin yaƙin domin kuwa mahaifinta, wanda sanannen farfesa ne, ya riƙe matsayin birgediya a rundunar sojin Biafra.
"Zan iya jure wa wahala. Zan iya kwana a dandaryar siminti mai sanyi kowanne lokaci," in ji ta.
Asalin hoton, Getty Images
Mrs Okonjo-Iweala ta aza harsashin gina sabbin azuzuwa a makaratar Chibok da mayakan Boko Haram suka cinna wa wuta a 2015
Sai dai macen da take yawan dariya idan 'yan jarida suna hira da ita ta ƙara da cewa: "Zan kuma iya yin barci a kan gadon gashi."
Irin wannan namijin kokari da tsayawa da dunga-duganta sun taimaka mata a yayin da take gudanar da sauye-sauye a Najeriya - kamar matakin da ta dauka na bayyana kudin da kowacce karamar hukuma take karba daga gwamnati a kowanne wata wajen gina hanyoyi da makarantu da asibitoci.
Masanin tattalin arziki Pat Utomi ya ce 'yan Najeriya ba su san adadin kudaden da shugabanninsu suke karɓa ba.
"Amma ta zo da tunanin wallafa dukkan abubuwan da ake ba su kuma hakan ya kunyata mutane da dama," in ji Farfesa Utomi.
Ta kaddamar da wani tsari da zai taimaka wajen fitar da dubban ma'aikata da 'yan fansho na bogi daga tsarin aikin gwamnatin kasar.
Sai dai a lokacin da gwamnati ta yi yunkurin cire tallafin man fetur a 2012, abubuwa ba su tafi yadda take so ba.
Ms Okonjo-Iweala ta ce ba za a iya ci gaba da biyan tallafin ba saboda kasar tana kashe kusan dala niliyan takawas a kansa a duk shekara, lamarin da a cewarta yake haifar da cin hanci.
Sai dai an tilasta wa gwamnati janye wannan matakin sakamakon yajin aikin da aka tsunduma a fadin kasar - a farkon wannan shekarar ne aka cire tallafin, inda gwamati ta yi alkawarin daidaita farashin man na fetur.
Wasu sun yi amannar cewa ko da yake sauye-sauyen nata suna da kyawu ga Najeriya amma ba masu dorewa ba ne.
'Kamar gudanar da harkokin gidanka ne'
Amma wata mai fafutukar kare hakkin mata a Najeriya Josephine Effa-Chukwuma ta ce ayyukan da Ms Okonjo-Iweala ta yi abubuwan sha'awa ne ganin cewa ba kasafai ake mutunta mata a kasar ba.
Ta shaida wa BBC cewa: "Ta sa mata suna alfahari da ita cewa mata a kasar da maza suka mamaye komai irin Najeriya suna iya yin aikin da ya dace ba kamar yadda 'yan-uba suke so ba."
"Ita mai gaskiya ce, mai yin komai a bayyane - abubuwan da ba a fiye samu ba a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya."
Ngozi Okonjo-Iweala tana bayani kan yaki da cin hanci
Masaniyar harkokin tattalin arzikin, wadda kuma ta kasance cikin daraktocin kamfanin Twitter, tana rike da mukamin shugaba a kamfanin alluran riga-kafi na Gavi kuma wakiliya ga Hukumar Lafiya ta Duniya kan yaki da cutar korona.
Cikin raha, ta taɓa cewa mata ba su cika shiga sha'anin cin hanci ba.
"Mata sun fi gaskiya, sun fi magana kai tsaye, sun fi mayar da hankali a kan ayyukansu, kuma ba su cika nuna jiji da kai a kan aikinsu ba. Ban sani ba ko batu ne da ya shafi mata kawai amma tafiyar da tattalin arziki wani lokaci tamkar tafiyar da arkokin gida ne," in ji ta, a hirar da ta yi da jaridar the Independent a 2006.
Ta ce mata na cikin wadanda za ta bai wa fifiko a mukaminta na shugabar WTO.