Waiwaye: Ɗalibi ya kashe kansa saboda budurwa, wani ya yanke al’aurarsa a Kano

Kamar kowane ƙarshen mako, wannan satin ma mun duba manyan labaran da suka faru a Najeriya daga Litinin 15 zuwa Asabar 20 ga watan Fabarairu.

An sace mutum 42 daga makarantar sakandare a Jihar Neja

Asalin hoton, TheCable

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da sace mutum 42 a wani hari da aka kai a daren Talata a makarantar sakandaren kimiyya ta kwana da ke garin Kagara a Jihar Neja.

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Bello ya ce an kwashe dalibai 27 da ma'aikata uku hadi da iyalansu guda 12.

Jim kaɗan bayan sace yaran ne kuma gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ba domin sako ɗaliban da malamansu. Shi ma Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta biya fansa ba.

Jihar Neja na cikin yankunan arewacin kasar da yan bindigar suke aika aikarsu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci jami'an tsaron kasar su yi duk mai yiwuwa domin ceto mutanen.

Sojojin Najeriya sun 'ƙwace gonar Shekau' a dajin Sambisa

Asalin hoton, PRNigeria

Sojojin Najeriya da ke yaƙi da Boko Haram a yankin arewa maso gabashi sun mamaye wata gona da suke ce ta Abubakar Shekau ce a dajin Sambisa.

Wani bidiyo da jaridar PRNigeria ta ce ta samu ya nuna yadda sojojin suka abka wa gonar da wasu kamar fararen hula suna kwasar amfanin gona.

A cikin bidiyon an ji sojojin na harbin bindiga suna yi wa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau shaguɓe cewa ya fito daga inda yake ɓuya.

"Shekau ina kake sarkin ɓaɓatu, ga mu a gonarka za mu yi sallar Juma'a a cikin Sambisa."

"Ba ka ce za ka yi shahada ba, ka fito mu barar da kai."

Jaridar PRNigeria ta ce sojojin bayan sun murƙushe wani hari a Dikwa sun kuma kama wasu masu taimakawa ƙungiyar ISWAP da bayanai.

NAFDAC ta amince da amfani da rigakafin korona na Oxford/AstraZeneca a Najeriya

Asalin hoton, UNIVERSITY OF OXFORD

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta amince da fara amfani da rigakafin cutar korona ta kamafanin Oxford/AstraZeneca a ƙasar.

Shugabar NAFDAC, Dr. Mojisola Adeyeye, ita ce ta bayyana hakan ranar Alhamis cikin wani jawabi da ta gabatar kai-tsaye ta talabijin.

Ta ƙara da cewa za a iya ajiye allurar a cikin yanayin sanyi daga 2 zuwa 8 na ma'aunin Celsius.

A cewarta, akwai rigakafi guda uku da ake kan tantancewa amma sakamkaon gwajin da aka yi a kan Oxford/AstraZeneca ya nuna cewa allurar na da tasiri sosai kan nau'in cutar wanda ya ɓulla a Birtaniya kuma ya shiga Najeriya.

Sai dai ta ce nau'in cutar da aka samu a Afirka ta Kudu bai ɓulla Najeriya ba zuwa yanzu.

Ɗalibin jami'a ya kashe kansa saboda budurwa a Jihar Jigawa

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Jami'ar Tarayya da ke Dutse FUD, a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin ɗalibanta da ake zargin ya kashe kansa bayan wata taƙaddama ta shiga tsakaninsa da budurwarsa.

Ana zargin matashin ya kashe kansa ne ta hanyar shan wani abu da ake zaton guba ce bayan budurwarsa ta zarge shi da kula wata daban ba ita ba.

To sai dai jami'ar ta FUD Dutse ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan al'amarin.

Daya daga cikin abokan karatun mamacin ya shaida wa BBC cewa al'amarin ya faru ne a unguwar Yalwawa inda marigayin da budurwar tasa da sauran ɗalibai ke haya, bayan ya koma gida daga makaranta.

Haka zalika abokin nasa ya ce matashin ya kashe kansa ne bayan da budurwar tasa da ke aji biyu a sashen tattalin arziki wato Economics, ta ce ta daina soyayya da shi a lokacin da suka je wani wurin cin abinci, a ranar masoya ta duniya a Lahadin da ta gabata, sakamakon ganowa da ta yi cewar yana kula wata bayan ita.

Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke al'aurarsa a Kano

Asalin hoton, FACEBOOK/KANO PPRO

Rundunar ƴan sandan Jihar Kanon Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi Mustapha Muhammad mazaunin unguwar Kurna layin Mallam Na Andi da ake zargin ya kashe kansa da kwalba.

Rudunar ƴan sanda tace matashin ya kashe kansa ne bayan ya kulle kansa a wani gida dake unguwar Masukwani a birnin Kano, ta hanyar cakawa kansa gilashin tagar ɗakin da ya shiga a gidan da ya kulle kansa.

Alamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan samun rahoto da ƴan sandan suka yi.

An kuma same shi ya yanke al'aurarsa.

Wasu yan uwansa sun ce yana fama da rashin lafiyar taɓin hankali.

Wani matashi ya kashe kansa a Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kanon Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani mutum Sabi'u Aminu mai shekara 60 da ake zargin ya rataye kansa a gidansa a Kano.

Rudunar ƴan sanda ta ce bayan samun labarin faruwar al'amarin ne suka isa gida kuma suka tafi da shi zuwa asibitin Sir Muhammad Sanusi, inda likitoci suka tabbatar musu da cewar ya rasu.

Ƴan sandan dai daga bayanan da suka tattara sun nuna cewa marigayin na sana'ar gyaran tayar mota da babur, a unguwar da yake da zama.

Abin fashewa ya kashe yara shida a Jihar Zamfara

Asalin hoton, Getty Images

Wani abin fashewa ya kashe aƙalla yara guda shida tare da jikkata wasu a ƙauyen Magamin-Diddi na Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ranar Lahadi.

Rukunin yaran da ya ƙunshi maza da mata 'yan shekara takwas zuwa 12, sun zaci ƙarfe ne kawai a lokacin da suka ga abin fashewar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗebo kara.

Huɗu daga cikinsu 'yan gida ɗaya ne.

Kwamishinan Tsaro na Zamfara, Abubakar Dauran, ya ce akwai yiwuwar jami'an tsaro ne suka jefa abin fashewar yayin wani hari da suke kaiwa kan 'yan fashin daji da suka addabi jihar.

Tuni aka yi jana'izar yaran kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, a cewar Abubakar Dauran.

Iyayen yaran sun shaida wa BBC cewa lamarin ya girgiza su sosai.

Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya WTO

Asalin hoton, Getty Images

Bayan shafe kimanin wata shida ba tare da shugaba ba, a ranar Litinin Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO ta nada tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya a matsayin shugabarta mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko.

Mrs Ngozi Okonjo-Iweala ta maye gurbin dan Brazil Alberto Azevedo wanda ya sauka daga mukamin a watan Augustan bara, gabanin cikar wa'adin mulkinsa.

Bisa tsari dai, sai duka kasashe 164 mambobin kungiyar sun amince kafin nada shugaba - don haka lokacin da Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta ƙi amincewa da nada Ngozi Okonjo-Iweala aka shiga kiki-kaka, har sai da shugaba Joe Biden ya hau karagar mulki a watan Janairu, kana ya sauya matsayin na gwamnatin Trump.

Ishaq Khalid ya duba mana kadan daga tarihin sabuwar shugabar ta Kungiyar Cinikayya ta Duniya, ga kuma rahotonsa.

Buhari ya nada ɗan shekara 40 a matsayin sabon shugaban EFCC

Asalin hoton, EFCC

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nada AbdulRasheed Bawa mai shekara 40 a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati ta EFCC.

An nada AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC ne watanni bayan sauke Ibrahim Magu wanda aka zarga da cin hanci.

A wasikar da ya aike wa Majalisar Dattawan ranar Talata, Shugaba Buhari ya ce AbdulRasheed yana da kwarewa a fannin bincike irin na zamba da almundahana da kuma halatta kudin haramun.

EFCC: Tsoffin jami'an gwamnatin Najeriya da za a tuhuma a shekarar 2021

Manyan jami'an Najeriya shida da suka yanke jiki suka faɗi yayin tuhumarsu

Sanarwar, wadda kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya sanyawa hannu, ta ce AbdulRasheed Bawa, mai shekaru 40, yana da digiri a fannin tattalin arziki da kuma digiri na biyu a fannin harkokin diflomasiyya da harkokin kasar waje.

Boko Haram ta kashe ƴan sanda a Yobe

Asalin hoton, Boko Haram

Rahotanni daga jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Bayamari inda suka kashe ƴan sanda da wasu mutanen gari.

Wani mazauni yankin ya shaida wa BBC cewa ƴan sanda huɗu maharan suka kashe da mutanen ƙauyen kusan mutum 10.

Bayamari na cikin ƙaramar hukumar Dapchi ne inda Boko Haram ta taɓa sace ƴan mata ɗaliban makarantar sakandare.

Kuma wasu bayanai sun ce an kashe ƴan sandan ne a yayin da suke ƙoƙarin kare mutanen ƙauyen daga ƴan ta'addan.