Tarzoma, agwagwa da zanga-zanga na cikin hotunan Afirka na mako: Daga 19 zuwa 25 ga watan Fabrairun 2021
Zababbun hotunan Afirka da 'yan nahiyar ta Afirka na wannan makon:

Asalin hoton, PA Media
An hango wannan agwagwar irin ta kasar Masar a cikin wani lambu da ke birnin London park ranar Laraba
Asalin hoton, AFP
Ranar Litinin, wannan yarinyar 'yar yankin Makonde na kasar Mozambique ta tsaya inda aka dauke ta a hoto a sansanin 'yan gudun hijira
Asalin hoton, SOPA Images
Wani dan kasar Masar da ke aikin sassaka a Iraki yana yi wa hoton hasumiya da ke wata kofa kwalliya ranar Litinin
Asalin hoton, EPA
Mahalarta bikin nuna kayan kawa na Milan Fashion Week a Italiya ranar Talata sanye da takunkumi. A karon farko, masu zane-zane 'yan asalin nahiyar Afirka su biyar sun samu damar baje kolinsu
Asalin hoton, AFP
Washegari a Morocco, wannan dan kasuwar yana zaune a shagonsa da ke binrin Marrakesh yana jiran kwastomomi
Asalin hoton, Getty Images
Mai tseren keke dan kasar Ethiopia Tsgabu Grmay yana fafatawa a gasar da ake kira UAE Tour a binrin Abu Dhabi da ke Hadaddiyar daular Larabawa ranar Litinin
Asalin hoton, Anadolu Agency
A ranar ce kuma, wannan mutumin da ke noman malafar kare a birnin Harare na kasar Zimbabwe, yana shirin kai su kasuwa
Asalin hoton, AFP
'Yan gudun hajirar da suka tsere daga riicin yankin tigray na kasar Ethiopia zuwa Sudan suna murnar cika shekara 46 da kafa jam'iyyar Tigray People's Liberation Front ranar Juma'a
Asalin hoton, AFP
Masu goyon bayan jam'iyyar hamayya a Jamhuriyar Nijar sun yi tarzoma Niamey babban birnin kasar ranar Alhamis, bayan an bayyana dan takarar jam'iyya mai mulki Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Wannan shi ne karon farko da gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata gwamnatin ta farar hula tun da aka bai wa kasar 'yancin kai
Asalin hoton, Gallo Images
A ranar ce kuma a Johannesburg, mambobin kungiyoyin ma'aikatan tarayya na Afirka ta Kudu suka soma zanga-zangar kasa baki daya domin jan hankalin gwamnati kan karuwar talauci da rashin daidaito.
Asalin hoton, Reuters
Kazalika ranar Alhamis, Senegal ta ci gaba da yi wa 'yan kasar allurar riga-kafin korona. Kasar ta bai wa makwabtanta uinea-Bissau da Gambia kusan kashi 10 na riga-kafin da ta sayo domin nuna musu 'yan uwantaka, a cewar shugaban Senegal
Asalin hoton, Reuters
Ranar Asabar, wannan yaron dan shekara biyar, dan gidan matukin motar tseren gudu na kasar Masar Tarek el-Erian, ya hau kan sitiyarin motar mahaifinsa.
Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka.