Salihu Tanko Yakasai: Ganduje ya tuɓe Ɗawisu daga muƙaminsa kan sukar Buhari

Abdullahi ganduje da Salihu tanko Yalkasai

Asalin hoton, @dawisu

Bayanan hoto,

Wannan ne karo na biyu da Ganduje ke korar Salihu daga aiki

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe Salihu Tanko Yakasai daga muƙamin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai bayan ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A jiya Juma'a ne Salihu, wanda aka fi sani da Ɗawisu a shafukan zumunta, ya yi kira ga gwamnatin jam'iyyar APC ƙarƙashin shugabancin Shugaba Buhari da ta "kawo ƙarshen matsalolin tsaro ko kuma su sauka daga mulki".

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Mohammed Garba ya fitar ta ce gwamnan ya ɗauki matakin ne saboda "kalaman rashin kan gado" da yake yi.

"Ya (Salihu) kasa tantancewa tsakanin ra'ayi na ƙashin kansa da kuma ra'ayin gwamnati kan abubuwan da suka shafi al'umma, saboda haka ba za a bar shi ya ci gaba da aiki da gwamnatin da ba ya goyon baya ba," sanarwar ta ambato Mohammed Garba yana cewa.

Ya ƙara da cewa korar ta fara aiki nan take.

Wannan ne karo na biyu da Ganduje ke ɗaukar matakin kora a kan mai taimaka masa ɗin na musamman. An kore shi a shekarar da ta gabata bayan ya soki Buhari kan ƙin yi wa 'yan ƙasa jawabi a loƙacin zanga-zangar EndSARS.

DSS ne suka kama ɗana - Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai ya ce jami'an tsaron farin kaya na DSS ne suka kama ɗansa Salihu Tanko Yakasai mai bai wa gwamnan Kano shawara kan yaɗa labarai.

Da yake tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, Tanko Yakasai ya ce binciken da 'yan uwansa suka yi ya tabbatar da cewa jami'an DSS ne suka kama shi kuma suka tafi da shi Abuja.

Sai dai, da BBC ta tuntuɓi shugaban 'yan sandan DSS na Kano, Alhassan Mohammed, ya musanta kama shi, yana mai cewa "ba mu ma san da kalaman da ake cewa Salihun ya yi ba".

Da aka tambayi Tanko Yakasai ko kamen nasa na da alaƙa da maganganun da ya yi (Salihu) game da gwamnatin Buhari, sai ya ce "DSS ɗin ne ya kamata su yi bayani".

"Mu dai ba mu san shi da aikata mummunan laifi ba, ba mu san shi da mummunar ɗabi'a ba, amma mun san shi da bayyana ra'ayinsa," in ji shi.

"Mun zaci ma masu garkuwa suka kama shi bayan an kasa jin ɗuriyarsa amma daga baya sai muka ji DSS ne suka kama shi," a cewarsa.

'Idan APC ba za ta iya ba ta sauka daga mulki - Ɗawisu

Asalin hoton, @Dawisu

Cikin wani jerin saƙonni a shafinsa na Twitter, Salihu Tanko Yakasai ya caccaki gwamnatin jam'iyyarsu ta APC game da matsalar tsaro, yana mai cewa "idan ba za ta iya ba ta sauka daga mulkin".

Sai dai tuni ya goge bayanan daga shafin nasa.

Ya ce: "A bayyane take gwamnatinmu ta APC ta gaza a kowane mataki, ta gaza yin babban abin da aka zaɓe mu mu yi, wanda shi ne kare rayuka da dukiyoyi.

"Kullum sai an samu matsalar tsaro a ƙasar nan. Wannan abin kunya ne! Ku yi maganin matsalar ko ku sauka daga mulki."

"Abin ya zama jiki, duk sanda wani bala'i ya faru mukan yi kuka, mu yi Allah-wadai, mu ƙirƙiri maudu'i (hashtag), gwamnati ta riƙa nuna tana yin wani abu a kai amma babu wata shaidar kare sake faruwar hakan, sannan a sake maimaitawa.

"Har sai zuwa yaushe? Ina waɗanda aka ɗaura wa alhaki? SMDH."