Hotunan ban mamaki da mutum-mutumin Amurka ya dauko daga Duniyar Mars
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech
Mutum-mutumin Perseverance na hukumar sararin samaniyar Amurka Nasa ya sauka a Duniyar Mars ranar 18 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:55 na dare agogon GMT, bayan tafiyar wata bakwai da ya shafe yanayi daga duniyar Earth.
Tun daga sannan, ya yi ta aiko hotuna masu kayatarwa daga inda ya sauka a duniyar, wato yankin Ramin Jezero, mai fadin kilomita 49 da zurfin mil 30 daga arewacin tsakiyar Jar Duniyar.
Ga dai wasu zababbun hotuna da mutum-mutumin ke aikowa, a yayin da yake ci gaba da neman wata alama ta ko an taba yin rayuwa a can, da kuma gano yadda yanayin kasa na duniyar yake da yadda sauyin yanayinta yake da kuma kwaso kasar wajen.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/MSSS
Bayanan hoto, Hoton farko na mutum-mutumin Perseverance da aka dauka da kyamara mai fito da hoto fes-fes da ke jikin Perseverance.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Wannan shi ne hoto na farko wanda ya fito fes mai kala da kyamarorin suka aiko bayan saukar mutum-mutumin.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/UArizona
Bayanan hoto, Ana iya hango Perseverance a wannan hoton mai kala a daidai inda ya sauka, kwana shida bayan saukarsa. Za ku iya ganin wasu bangarori biyu masu haske daga gefen mutum-mutumi.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Perseverance yana dauke da wasu manyan na'urori na kimiyya da zu su tattaro bayanai a kan yanayin kasar duniyar, yanayin samaniyarta da kuma yanayin, muhallinta. Kyamarar da ta dauki wannan tana makale ne a kan turken da ke jikin mutum-mutumin.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Nan hoton wani sashe na jikin na'urar ne da zai dinga gano alamomin sinadarai.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Akwai kuma wata kyamara da ke daukar hotuna na kurkusa na duwatsu da kasar wajen.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU/MSSS
Bayanan hoto, Wannan ne hoto na farko da kyamarar ta dauka a zagaye. An dauka da kyamarar Mastcam-Z, da kuma wata da ke jikin na'urar. An hade bidiyon ne daga duniyar Earth daga hotuna 142 daban-daban.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU/MSS
Bayanan hoto, Wannan dutsen an sa masa suna "harbour seal", saboda wasu dalilai.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU/MSSS
Bayanan hoto, Wannan hoton na nuna yawan bayanan da ake samu daga abin da kyamarorin ke dauka.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU
Bayanan hoto, Shi kuma wannan hoton an dauke shi ne da idon hagu na kyamarar Mastcam-Z. Kyamarorin hagu da na daman suna kusa da juna kuma suna kallon waje daya, inda suke dauko yanayin d ko a zahiri haka za a gani.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU
Bayanan hoto, Bayan kwanaki biyu, sai aka dauki wannan hoton da waccar kyamarar dai, kuma wannan hoton shi aka zaba a matsayin "hoton mako" a cikin mako na biyu na saukar Perseverance a Mars.
Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech/ASU
Bayanan hoto, Wannan hoton kuma idon dama na kyamarar Mastcam-Z ne ya dauke shi, wani tsohon yanki ne na waje mai damshi a Jezero, wanda ya ware daga ainihin yankin sakamakon zaizayar kasa tsawon lokaci. Kasar da ke nan wajen na daya daga cikin manyan ayyukan kimiyya da ake son mutum-mutumin ya yi don gano rayuwar farko da aka yi a wajen.
Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Hotunan farko da suka fara isowa duniyar Earth na saukar na'urar ce a Mars.
Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Wannan hoton ma an dauke shi a lokacin saukar. Inda ya rage kilomita 11 na'urar ta dira kasa, a lokacin da lemar taimaka wa wajen saukata ta bude.
Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Wannan hoton na nuna dandaryar kasar duniyar Mars ne da ke kasan na'urar.
Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech
Bayanan hoto, Ga wani hoton ma da aka dauka yana kallon ramin Jezero a yayin da na'urar ke sauka.
An zuba tallafin kudi da zai sa Perseverance ta shafe shekara daya a Mars tana aiki, wanda ya yi daidai da shekara biyu a Earth.