Ba a yi wa Tinubu kora da hali a APC ba – Farouk Adamu Aliyu

Tinubu

Asalin hoton, Tinubu Twitter

Bayanan hoto,

Tinubu ya ce aikin sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar da ake yi a lokacin a jihohin ƙasar baki ɗaya ba shi da wani tasiri

Ƴan jam'iyyar APC mai mulki sun musanta cewa wani ɓangaren jam'iyyar na yi wa daya daga cikin jiga-jigan APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu kora da hali.

Wani al'amari da ya fito da zaman tankiya a jam'iyyar a baya-bayan nan dai shi ne yadda Bola Tinubu ya fito ya bayyana ƙorafinsa dangane da shirin sabunta rijista da jam'iyyar APC ta gudanar.

A hirarsa da Usman Minjibir na BBC Hausa, Hon Farouk Adamu Aliyu wanda jigo ne a jam'iyyar ya ce babu ƙamshin gaskiya a kan cewa ana ƙoƙarin yi wa Bola Tinubu kora da hali daga APC.

Ya ce: "Ai ba za mu so a ce Tinubu ya bar jam'iyyar APC ba. A jam'iyyar APC ba wanda ya isa ya raina Tinubu, ba wanda ya isa ya ce Tinubu ba kowa ba ne, ba wanda ya isa ya raina irin gudunmowar da ya baiwa jam'iyyar APC har ta kai ga mulki a shekarar 2015 da 2019."

Duk da cewa an daɗe ana raɗe-raɗin cewa gwamnatin Shugaba Buhari na yi wa Tinubu bi-ta-da-ƙulli, Farouq Adamu ya ce zancen ƙarya ce tsagwaronta.

"Babu jam'iyyar da za ta so ta rabu da Tinubu, ba gaskiya ba ne babu abin da ake yi wa Tinubu na wulaƙanci ko yi masa wani abu na ba daidai ba.

Wasu na ganin sabunta katin da ake yi na jam'iyyar APC a faɗin kasar wani shiri ne da ke nuna inda jam'iyyar za ta karkata a zaɓen 2023 na irin mutanen da za ta zaɓo su yi shugabanci.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai Farouq Adamu ya ce ai jam'iyya ce ba dole babu wanda za a sa wa igiya a jawo shi, idan kowace jiha ta Najeriya ba ta son shiga jam'iyyar APC yaya za ka yi da ita?

"Wannan ya rage wa jagororin da suke so su nemi buƙata a APC su je su nemo jama'a su sa su yi rijista. Ba gaskiya ba ne cewa akwai wasu da ake so su fita daga jam'iyyar nan. Mu ba mu ƙi ba ma gaba ɗaya ƴan Najeriya su zama ƴan APC," a cewarsa.

Ƴan Najeriya da dama dai a shekarun bayan nan na mulkin Shugaba Buhari na yawan koka wa kan mulkin jam'iyyar APC kan taɓarɓarewar tsaro a sassan ƙasar da dama da kuma jawo rarrabuwar kawuna tsakanin kudu da arewacin ƙasa, don haka wasu za su yi tababar batun na Farouq Adamu.

Amma ya kare maganar da cewa: "Babu yadda za a yi gwamnati kowace iri ce ko da ta PDP su kawo abin da zai rarraba kawunan al'umma. Kuma su masu mulkin nna rantsuwa fa suka yi kan cewa za su kare martabar ƴan Najeriya, amma bambance-bambancen addiniai da yaruka ka sawa ba a rasa irin wadannan abubuwa."

"Amma ina tabbatar da cewa babu wani abu da gwamnatin APC ke yi don kawo wanna matslaar rabuwar kai," a cewarsa.

Asalin hoton, @APCNIGERIA

Ya ba da misali da abin da ya faru na rikicin ƙabilanci a Kasuwar Sasa ta jihar Oyo, inda rikicin ƙabilanci ya ɓarke amma ba a samu mayar da martani a arewa ba, inda ya ce hakan ya biyo bayan sasanci da gwamnatin APC ta dinga yi ne da kwantar da hankulan mutane.

Yadda zargin ya samo asali

Tun a farkon watan Fabrairu ne sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APCn sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigonta Bola Ahmed Tinubu.

Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ce aikin sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar da ake yi a lokacin a jihohin ƙasar baki ɗaya ba shi da wani tasiri.

"Sabunta rijistar da jam'iyyar ke yi tamkar a sanya ɗaya ne kana kuma a cire ɗaya, don haka ni ina ganin ba wata ƙaruwa ba ce'', a cewar Tinubu.

Wannan kalamin ya sa wasu ƴaƴan jam'iyyar na cewa da walakin goro a miya, kuma alama ce da ke nuna cewa bai ji daɗin abin da ake yi ba, saboda a cewarsu, aikin rijistar zai iya rage masa ƙarfin mamayar da ya yi wa jam'iyyar, da kuma tasirin da yake da shi a cikinta.

Sai dai masana, irin su Malam Kabiru Sufi na kwalejin share fagen shiga jami'a ta jihar Kano na cewa fitar irin wɗannan kalamai daga bakin Bola Tinubu a matsayinsa na jagora, duk kuwa da cewa yana da damar yi wa jam'iyyar gyara tun a matakin shirin rijistar, na nuna cewa akwai ɓaraka.

Har zuwa yanzu dai Mista Tinubu bai fito ya ce yana neman shugabancin Najeriya ba, amma tuni wasu masoyansa suka fara tallata shi.

Ko da yake wasu ruwayoyin na nuna cewa wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC daga arewacin Najeriya ba sa goyon bayan haka.