Coronvirus a Najeriya: An yi wa Buhari allurar rigakafin Korona

Asalin hoton, Facebook/FEMI ADESINA
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi allurar rigakafin korona a ranar Asabar.
Likitan shugaban ne Dr Shu'aibu Rafindadi ya yi wa shugaban allurar da misalin ƙarfe 11:53 a fadarsa da ke Abuja.
Shi ma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo an yi masa allurar.
Kazalika, an bai wa shugaban da kuma mataimakinsa katin shaidar karɓar allurar.
A jawabinsa bayan karɓar allurar, shugaba Buhari ya yi kira ga ƴan Najeriya su fito domin a yi masu allurar.
Shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona a Najeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya ƙasashen waje.
A ranar Juma'a ne Najeriya ta ƙaddamar da allurar rigakafin korona a ƙasar, inda aka fara yi wa likitoci kafin shugabanni da kuma sauran ƴan ƙasa.
Allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca Najeriya ta karɓa a ranar Talatar makon da ya gabata.
Adadin yawan riga-kafin

Asalin hoton, Presidency
Allurar rigakafi kusan miliyan huɗu Najeriya ta karɓa daga wani ɓangare na rigakafi miliyan 16 da shirin COVAX ya tsara ba kasar.
Shirin Covax ya shafi tabbatar da kowace kasa a duniya ta samu nata kaso na rigakafin korona.
Wannan kaso ne na farko da Najeriya za ta karɓa daga cikin miliyan 16 da za ta samu ƙarƙashin inuwar Covax a watanni masu zuwa.
Gwamnatin ƙasar kuma ta ce ta tsara yi wa akalla kashi 70 na ƴan Najeriya da suka cancanci a yi musu riga-kafin wato wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa sama a cikin shekaru biyu.
A bana Najeriya na fatan yi wa kashi 40 na ƴan kasarta rigakafin da kuma kashi 30 a 2022.
Najeriya ta kasance kasa ta uku a yankin Afrika Ta Yamma da suka ci moriya tallafin alluran riga-kafin karkashin shirin COVAX, baya ga Ghana da Cote D'Ivoire.






