Senegal: Zanga-zanga na ci gaba da fantsama zuwa wasu jihohi

Zuwa yanzu mahukunta sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 4,

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zuwa yanzu mahukunta sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 4,

Wani ɗalibi matashi ya zama mutum na biyar da aka kashe a Senegal yayin zanga-zangar da ta biyo bayan kama jagoran adawa a ƙasar Ousmane Sonko ranar Laraba.

An kashe shi ne ranar Asabar a arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a garin Diaobe da ke kudancin ƙasar.

Bayanai na cew ana ci gaba da banka wa gine ginen gwamnati wuta a jihohin kasar, ciki har da babban birnin Dakar, inda lamarin ya fi ƙamari.

A yanzu lamarin ya isa wasu manyan biranen ƙasar uku, da suka haɗar da Sedhiou da Kolda da kuma Diaoube dukkansu a yankin kudancin ƙasar.

Ganin yadda lamarin ya yi ƙamari, ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ta yammacin Afirka, ECOWAS ko kuma CEDEAO ta yi kira kamar sauran kungiyoyi na kasa da kasa da a mayar da takobi kube.

Zuwa yanzu mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutum biyar, sannan wasu da dama kuma sun jikkata, sakamakon zanga-zangar da aka soma a ranar Laraba.

Abin da ya haifar da zanga-zangar

Ousman Sonko

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ousman Sonko

Kama dan adawar kasar Ousmane Sonko na jam'iyar MDD wato 'Movement for the Defence of Democracy da hukumomin ƙasar ta Senegal su ka yi shi ne ummal iba'issan wannan babban hargitsi.

A watan jiya ne aka soma zargin ɗan adawar da yi wa wata ma'aikaciyar otel fyade, yayin da take yi masa tausa, zargin da tuni ya fito ya musanta.

Jam'iyar shi ta MDD ta danganta zargin da wani ƙulumboton siyasa, don hana shi tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar da ake tunkara.

Ana dai sa ran cewar ranar Litanin din nan Sonko zai bayyana a kutu game da zargin da ake mashi.

Wasu bayanai na cewa kiran masu zanga zangar a matsayin 'yan ta'adda da ministan watsa labaran ƙasar ya yi a ranar Jumma'a ya ƙara tunzura masu zanga zangar, inda a yanzu suke kiran shugaba Macky Sall ya sauka ɗungurungum.