Ƴan majalisar Bauchi na farautar wanda ake zargi ya yi wa ƴar shekara 7 fyaɗe

rape victim

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar Bauchi ta shiga farautar wani da ake zargi ya yi wa wata yarinya yar shekara bakwai fyaɗe.

Wasu ƴan majalisar sun yi zargin cewa an bayar da mutumin mai shekara 45 beli bayan kama shi.

Lamarin ya faru ne a Faggo da ke ƙaramar hukumar Shira a jihar ta Bauchi.

Ɗan majalisar da ke wakiltar yankin Honarabul Bello Muazu Shira, wanda ya gabatar da kudirin gaban majalisa ya yi kiran a gaggauta kama mutumin kan zargin yi wa ƴar shekara bakwai fyaɗe.

"Ya yi wa yarinyar barazana da makami ya yi mata fyaɗe," in ji shi

Ɗan majalisar ya shaida wa BBC cewa majalisa ta kafa kwamiti domin tabbatar da an kama mutumin.

Ya ce sun kama hanya zuwa Shira kuma a cewarsa "zamu ta fi har garin Faggo inda yarinyar take."

Ya kuma ce za su tattauna da shugaban ƙaramar hukumar Shira da jami'an ƴan sanda domin tabbatar da an kama mutumin.

Sai dai ɗan majalisar ya ce ba su san inda mutumin da ake zargi yake ba a yanzu. Amma ya jaddada cewa majalisa za ta tabbatar da an gurfanar da shi a gaban shari'a domin zama darasi ga masu aikata fyaɗe.

Matsalar fyaɗe dai musamman ga yara ƙanana ta zama ruwan dare a Najeriya. Kuma an sha bayar da rahoton fyaɗe a jihar Bauchi

Wannan ne ya sa gwamnatin jihar Bauchi ta kafa wata doka da ta kira VAPP wadda a turance ake kira Violence Against Persons Prohibition, ta kuma tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyaɗe.

Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyaɗe, da kuma ɗaurin shekaru 20 ga waɗanda suka yi wa mace daya taron dangi.

Hukumomin ƴan sanda a jihar sun ce sun sha samun rahotannin aikata fyaɗe a jihar.