Gwamnatin Kaduna ta ce babu ɗalibin firamare da aka sace

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babu ɗalibi ko ɗaya da aka sace a makarantar firamare a kauyen Rema da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
Gwamnatin ta tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin. Amma sanarwar ta tabbatar da kai hari makarantar kuma an tafi da wasu malaman makarantar guda uku.
A cewar gwamnatin, yara 'yan firamaren da tun farko aka yi zaton 'yan bindiga sun sace a yayin farmakin da suka kai makarantar firamaren kauyen Rema a karama hukumar Birnin Gwari, a yanzu an gano su.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewa "yanzu haka babu wani ɗalibi da ke hannun 'yan bindigar sai dai malamai.
Ya ce bayan bin sawu da bincike an gano babu ɗalibin da ya salwanta, sannan kuma gwamnatin ta ce malamai uku suna hannun 'yan bindigar.
Al'ummar kauyen Rema sun ce suna cikin fargaba da tashin hankali kasancewar 'yan bindigar ba su da tabbas za su iya koma musu.
Wani mutum da 'ya'yansa suka koma gida bayan tserewar maharan, ya ce an sace masa shanu biyu sannan ya ce akwai fargaba sun tafi da wani makocinsa.
Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro suka daƙile yunkurin sace wasu ɗalibai a wata makaranta a jihar ta Kaduna.
Kuma wannan ne karon farko da aka kai hari wata makarantar firamare a Najeriya ko da yake an sha kai hare-hare makarantun sakandire inda wasu alƙalumma suka ce kusan ɗalibai 800 aka sace.
Har yanzu hukumomi na ci gaba da kokarin kubutar da ɗaliban kwalejin horas da ma'aikatan gandun daji fiye da talatin da har yanzu suke hannun 'yan bindigar.
Manazarta na ci gaba da nuna fargaba game da makomar ilimin boko musamman a arewacin Najeriya.
Masanan na ganin tilas sai hukumomi sun ƙara hubbasa don kaucewa durkushewar harkokin ilimin da kuma tattalin arziki da kuma noma wanda a kullum ke fuskantar mummunar barazana.