Mutum hudu sun mutu, 189 na kwance asibiti a Kano

Mutum hudu sun mutu, 189 na kwance asibiti a Kano

Latsa hoton sama domin sauraren rahoton Khalipha Dokaji

Hukumomin lafiya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum hudu sakamakon bullar wata cuta a jihar.

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana na cibiyar dakile cutuka masu yaduwa da ke asibitin Muhammadu Abullahi wasai, Dakta Bashir Lawal ne ya tabbatar wa BBC .

Dakta Bashir ya ce tun da farko sun samu labarin bullar wata cuta da ba a kai ga gano ta ba, wadda mutanen da ta kama ke fitar da jini da amai da gudawa.

Hakan ya sa suka yi tsammanin cutar lassa ce saboda alamominsu sun yi kama da juna, amma bayan gudanar da bincike an gano ba Lassa ba ce.

Kwararren likitan ya ce "Mutum hudu sun mutu dalilin wannan cuta, ta kashe biyu a asibiti da kuma kashe mutum biyu da suke jinya a jida.

"Ya zuwa yanzu cutar ta kama mutum 189 wadanda suke asibitoci mabambanta da aka ware domin yaki da wannan cuta" in ji likitan.

Hukumomin lafiya a jihar sun ce dukkan asibitocin da ke jihar za su iya karbar masu fama da wannan cuta domin ba su agajin gaggawa.

A binciken da hukumomin suka gudanar sun gano cewa wannan cuta ba mai yaduwa ba ce, shi yasa masu fama za a iya kwantar da masu fama da ita a sauran asibitoci.

Wannan al'amari dai ya fara aukuwa ne a makon da ya gabata, inda rahotanni suka ce ya faru ne bayan shan wani lemu dan tsami aka barke da Fitsarin jini da amai.