Sayyada Rabi'atu Haruna: Ana jimamin rasuwar matar da ta yi wakar 'Mai daraja Annabi Ma'aiki'

Daga hagu zuwa dama: Sayyada Rabi'atu, Sharif Mua'zu da kishiyarta

Asalin hoton, Sharif Mu'azu

Bayanan hoto, Daga hagu zuwa dama: Sayyada Rabi'atu, Sharif Mua'zu da kishiyarta

Musulmi a Najeriya da ma wasu kasashen duniya sun fada cikin jimamin rasuwar Sayyada Rabi'atu Haruna, matar nan da ta yi fice wajen wakokin yabon Annabi Muhammad (SAW).

Mijinta Sharif Mu'azu ya shaida wa BBC cewa a ranar Talata ne mawakiyar ta rasu a gidanta da ke Rigasa a birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan ta yi jinyar mako uku.

Ya ce an yi jana'izarta da yammacin ranar ta Talata.

A cewarsa mutuwar Sayyada Rabi'atu ta yi matukar girgiza shi da iyalinsa yana mai yin addu'ar Allah ya jikanta.

Sharif Mu'azu ya bayyana mai dakin nasa a matsayin mutuniyar kirki wadda ya ji dadin zama tare da ita.

Sayyada Rabi'atu ta bar 'ya'ya biyu a duniya.

Ta yi wakokin yabon annabi wadanda suka hada da 'Sayyidin Nasi Karimi', 'Mai daraja Annabi Ma'aiki', 'Zahra'u Fadima', 'Shukriyya Sajida', da wasu da dama.

Masu sha'awar wakokinta da ma sauran Musulmi musamman a shafukan sada zumunta sun yi matuka kaduwa da jin rasuwar mawakiyar.

Isa Usman ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Sayyada Rabi'atu yana mai yin addu'ar Allah Ya sa ta kasance "bakuwar Muhammadur RasululLah Sallallahu Alayhi Wa Sallam."

Kauce wa Twitter
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter

Shi ma Adamu Aliyu Shu'aibu ya yi mata fatan samun rahamar Allah sannan ya ce yana "kaunar wakokinta irin su 'Na yi dace na rike soyayyar ma'aiki, da 'Abin dogaro Muhammadu' da kuma Karimiya"

A nasa bangaren, Bilya Hamza Dass, ya yi alhini sannan ya bayyana daya daga cikin wakokinta da ya sani.