Hotunan Afrika daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Maris 2021

Wasu zababbun hotunan nahiyar Afrika na wannan makon.

Wasu jakunan dawa a yammacin ranar Lahadi suna tsallakawa titi, tare da tilastawa masu mota dakatawa sai sun tsallaka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu jakunan dawa a yammacin ranar Lahadi suna tsallaka titi tare da tilasta wa masu mota dakatawa sai sun tsallaka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani dan Gambia mai suna Toure mai sana'ar kwaso gishiri daga kasan kogin Retba a Senegal a ranar Talata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An fi sanin sa da kogin "Pink Lake" saboda furannin da suke ciki wadanda suke sauya masa launi

Asalin hoton, Christopher Furlong

Bayanan hoto,

A ranar Litinin wasu masu zane sun zana hoton wata yarinya Ansha mai shekara 12 a Habasha.....

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zanen ya matukar daukar ido ya kuma kawata bakin ruwan da aka yi zanen a arewacin Ingila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Talata, wani dan sanda rungume da wata 'yar zanga-zanga, a zanga-zanga mafi tsari da aka yi a Algeriers babban birnin Algeria.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar na bukatar duk wani mai rike da mukami a gwamnatin kasar ya sauka..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar neman tallafi ga daliban jami'a a Johannesburg sun yi cuncurundo a manyan titinan birnin a ranar Litinin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani mutum na kirga kajinsa a wata kasuwa a Makelle babban birnin yankin Tigray na Habasha a ranar Talata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A irin wannan ranar a jihar Gedaref da ke gabashin Sudan, wani yaro na jika fuskarsa da ruwa a kogin Atbarah.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A Tanzaniya an wayi gari da Labarin mutuwar shugaban kasar John Magafuli wanda ya mutu yana da shekara 61 a duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

On Wednesday mourners gather at the Olympic stadium in Abidjan, Ivory Coast, to remember the late Ivory Coast Prime Minister Hamed Bakayoko...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mai kidan rege Alpha Blondy na daga cikin wadanda suka yi waka domin tunawa da marigayin wanda mutu yana da shekara 56 bayan kamuwa da cutar kansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu juyayi a Afrika Ta Kudu suna tunawa da Sarki Zulu Zwelithini wanda ya mutu yana da shekara 72 bayan fara da ciwon siga